Putin ya sake barazanar amfani da makaman nukiliya kan ƙasashen yammacin duniya

0
1390
Putin ya sake barazanar amfani da makaman nukiliya kan ƙasashen yammacin duniya

Putin ya sake barazanar amfani da makaman nukiliya kan ƙasashen yammacin duniya

Shugaba Vladimir Putin ya gargaɗi Amurka da ƙawayenta akan cewar Moscow na duba yiyuwar maida martani da makaman nukiliya matuƙar suka bari Ukraine ta kai hari cikin Rasha ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da aka ƙera a ƙasashen yammacin duniya.

A gargaɗin baya-bayan nan daga jerin waɗanda ya yi a baya, a jiya Laraba, Putin ya ƙara zayyano jerin dalilan da za su sabbaba rasha yin amfani da makaman nukiliya.

A cewarsa, haka za ta iya kasancewa, wajen maida martani ga wani babban harin da aka kawo cikin Rasha daga ketare ta hanyar amfani da jiragen saman yaki ko makami mai linzami ko jirgi marasa matuki.

KU KUMA KARANTA:Putin ya fara wa’adi na biyar a karagar mulkin Rasha

“Zamu zartar da hukuncin bai daya kan duk kasar dake da makamin nukiliya kuma take gaba da Rasha da ta taimaka wajen kai mana farmaki” a cewar Putin.

Idan har Putin ba da gaske yake yi ba, kamar yadda Ukraine da wasu magoya bayanta suka zata, to lokaci yayi da kasashen yamma zasu kara yawan taimakon sojin da suke baiwa Kyiv ba tare da la’akari da barazanar dake fitowa daga Moscow ba.

Idan har hakan ta kasance da gaske, to akwai hatsari-kamar yadda Moscow ta sha nanatawa kuma Washington ta shaida hakan-yakin na iya rikidewa zuwa yakin duniya na uku.

Leave a Reply