Paris 2024: ‘Yansandan Faransa suna ƙarfafa tsaro saboda ƙasashe masu adawa da juna

0
60
Paris 2024: 'Yansandan Faransa suna ƙarfafa tsaro saboda ƙasashe masu adawa da juna

Paris 2024: ‘Yansandan Faransa suna ƙarfafa tsaro saboda ƙasashe masu adawa da juna

Shugaban tawagar ‘yan wasan ƙasar Iraqi ya ce shugabannin Olympics sun yi watsi da buƙatar su cewa ka da a cira tutar Isra’ila a kusa da ta Iraqi a lokacin wasannin Paris.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar maza ta Iraqi ta lallasa Ukraine da ci 2-1 a birnin Lyon a ranar Laraba kana ta sha kashi a hannun Argentina da ci 3-1 a ranar Asabar.

“Yayin da muka isa filin wasa na Lyon a ranar Laraba, mun ga an kafa tutar Iraqi kusa da ta Isra’ila,” duk da cewa ƙungiyar Isra’ila ba ta da wani wasa da za ta yi a Lyon, in ji Herda Raouf, yana fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Raouf, wanda bai yarda da hallacin kasar Isra’ila ba kuma yake marawa kasar Falasdinu baya, ya kara da cewa tawagarsa ta bukaci wakilin kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya (OIC) da ta sake wa tutar Isra’ila wuri amma an yi buris da bukatar su.

KU KUMA KARANTA:Abin da ya sa ba ma ɗaukar alƙalan wasa daga Najeriya – FIFA

A cewar Raouf, wakilin na kwamitin ya ce an shirya tutocin kungiyoyin ‘yan wasan kwallon kafar mata da mazan ne bisa tsarin harafin fari na kowace kasa.

Raouf ya kara da cewa, tawagarsa ta kara tura kin amincewarta a hukumance ta sakon imel zuwa ga IOC a kan bukata wannan kafin wasanta da Argentina, amma aka kuma sake fatali da ita.

Dakarun tsaron Faransa suna kallon wasan Ukraine da Iraqi da kuma wasan Isra’ila da Mali da aka yi su a ranar Laraba a matsayin masu tattare da hadari.

Kimanin jami’an ‘yan sandan Faransa dubu daya ne aka jibge domin bada tsaro a wasan Isra’ila da Mali, inda ‘yan kallo su ka daga tutar Falasdinu da ta Irsa’ila.

Kwamitin Olympic na kasar Falasdinu sun rubutawa IOC a makon da ya gabata cewa ta hana ‘yan wasan Isra’ila shiga gasar Olympics a Paris saboda yakin Gaza, bukatar da aka yi fatali da shi.