Paris 2024: An hana ‘yar Najeriya damar fafatawa a gasar tseren mita 100
‘Yar tseren Najeriya, Favour Ofili, ta bayyana cewar ba za ta fafata a gasar tseren mita 100 a gasar Olympics ta birnin Paris ba saboda gazawa a fannin gudanarwa tsakanin hukumar kula da ‘yan wasan motsa jiki ta Najeriya da kwamitin shirya gasar Olympics ta ƙasar.
Da take bayyana takaicinta a jerin saƙonnin X da ta wallafa a jiya Talata, Ofili ta tuhumi gaskiya da amanar hukumomin 2, sannan ta buƙaci a gudanar da bincike a kan asarar wannan damar.
Ofili wacce tsohuwar ‘yar wasar guje-guje da tsalle-tsalle ce ta jami’ar jihar Legas ta bayyana fatan shigar da ita a gasar tseren mita 200.
KU KUMA KARANTA;Paris 2024: ‘Yansandan Faransa suna ƙarfafa tsaro saboda ƙasashe masu adawa da juna
An ruwaito abin da ta wallafa na cewar, “ina matuƙar takaicin cewar yanzun nan aka shaida mini cewar ba zan fafata a gasar tseren mita 100 ta wannan wasannin olympics ba. Na cancanta, amma jami’ai a hukumar AFN, mai kula da ‘yan wasan motsa jikin Najeriya da na kwamitin shirya gasar Olympic na Najeriya sun gaza shigar da suna na. Na yi aiki tsawon shekaru 4 domin samun dama. Don me haka za ta faru?”
Duk da cewar ta cancanta ta fafata, Ofili ta bayyana cewar jami’an ba su shigar da sunanta ba, matakin da ya janyo maimaituwar irin abin da ya faru a gasar wasannin Olympics da ta gabata, ta birnin Tokyo a shekarar 2020.
Sai dai Ministan Bunƙasa Wasannin Najeriya, Sanata John Owan Enoh, yace zai binciki yadda aka tsame sunan ‘yar wasan motsa jikin, daga gasar na bana dake gudana yanzu haka a birnin Paris.