NYSC za ta ba da satifiket ga ‘yan hidimar ƙasar da ‘yan bindiga suka sace

0
71
NYSC za ta ba da satifiket ga 'yan hidimar ƙasar da 'yan bindiga suka sace

NYSC za ta ba da satifiket ga ‘yan hidimar ƙasar da ‘yan bindiga suka sace

Hukumar yi wa ƙasa hidima ta ƙasa (NYSC) ta kammala shirin bayar da satifiket ga masu yi wa ƙasa hidima na tsawon shekara ɗaya, bayan da aka yi garkuwa da su.

‘Yan bindiga sun sace masu hidimar ƙasar ne a jihar Zamfara suna kan hanyar su ta zuwa Sakkwato, inda aka tura su sansanin horo na makonni uku a ranar 17 ga Agusta, 2023.

Waɗanda abin ya shafa dai sun haɗa da Daniel Etim Bassey (Dan karamar Hukumar Uruan, wanda ya kammala Jami’ar Najeriya, Nsukka); Uyo, Obong Victor Udofia (Ikono LGA, Jami’ar Uyo); Sabbath Anyaewe Ikan (Eastern Obolo LGA, Akwa Ibom Polytechnic); Abigail Peter Sandy (Abak LGA, Maurid Polytechnic); Glory Etukudo Thomas (Eket LGA, Heritage Polytechnic); Emmanuel Esudue (Urue Offong Oruko LGA); Victoria Bassey Udoka (Ini LGA, Jami’ar Uyo); Solomon Bassey Daniel (Itu LGA, Akwa Ibom Polytechnic);

Suna tafiya ne a cikin wata motar bas ta kamfanin sufuri na Akwa Ibom (AKTC) lokacin da aka yi musu kwanton bauna.

KU KUMA KARANTA:An ceto sauran ɗaliban Jami’ar Gusau da ’yan NYSC da ke hannun masu garkuwa

Daga baya kuma an sake su daya bayan daya , inda na karshen ya samu ‘yanci a wannan makon.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, a jiya Juma’a, Darakta Janar na Hukumar NYSC , Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya ce za a ba wa wadanda abin ya shafa takardar shaidar kammalawa.

Ahmed ya ce bayan duk sun shafe shekara a hannun wadanda suka yi garkuwa da su, ba za a iya sake tura sunayen su don sake shirin ba.

Leave a Reply