NNPP ta nesanta kanta da shirin Kwankwaso na komawa APC
Daga Jameel Lawan Yakasai
Sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dr. Ogini Olaposi, ya bayyana cewa shirin komawa jam’iyyar APC ba na jam’iyyar NNPP ba ne, sai dai na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyar Kwankwasiyya.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas, bayan da Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a 2023, ya sanar a karshen mako cewa shi da magoya bayansa sun shirya shiga jam’iyyar APC mai mulki.
Olaposi ya ce wannan mataki ya tabbatar da cewa Kwankwaso da ƙungiyarsa ba su cikin jam’iyyar NNPP tun bayan da aka kore su saboda zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.
Ya kara da cewa duk wani tattaunawa da za a yi da Kwankwaso daga yanzu za ta kasance a matsayin nasa mutum ɗaya, ba a madadin jam’iyyar ba.
KU KUMA KARANTA: NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin Ƙofa daga jam’iyyar
Ya bayyana cewa NNPP za ta ci gaba da tsara tsarin cikin gida domin shiryawa zaben 2027, bayan rikici da shari’o’in da magoya bayan Kwankwaso suka haddasa.
A cewar Olaposi, yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin NNPP da Kwankwasiyya ta ƙare ne bayan zaɓen 2023, inda daga baya Kwankwaso ya fara yunƙurin kwace jam’iyyar.
Ya ce yawancin magoya bayan Kwankwaso a Kano sun riga sun shiga APC tun da dadewa, kuma yanzu babu jam’iyyar siyasa da yake da ita. Olaposi ya jaddada cewa duk wata tattaunawa da Kwankwaso ke yi, hakki ne nasa a matsayin ɗan ƙasa, amma ba a madadin NNPP ba, domin a hukumance har yanzu an kore shi daga jam’iyyar.









