NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa Chaina da Japan

0
81
NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa Chaina da Japan

NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa Chaina da Japan

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya ce ya fitar da gas zuwa ƙasashen Japan da Chaina domin sayarwa.

Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ambato Shugaban Hukumar tace mai na NNPC, Segun Dapo, na cewa hakan na daga shirye-shiryen kamfanin na kasancewa mai samar da nagartaccen makamashi a kasuwannin duniya.

Dapo ya ce ɓangarensa ya samu gagarumin haɗin kai daga ɓagarorin kamfanin NNPC na gas da kuma na sufurin jiragen ruwa.

A sakamakon haka, jirgin farko ɗauke da gas ɗin sayarwa ya bar Najeriya zuwa Japan a ranar 27 ga Juni, 2024.

“A shekarar 2021 NNPC ya fara harkar kasuwancin gas kuma kawo yanzu ya fitar da jirager ruwa sama da guda 20 na gas zuwa yankunan Asiya da turai.

KU KUMA KARANTA: Gayawa ‘yan Najeriya gaskiya gamaida tallafin man fetur – Bode George

“Hakan zai ba kamfanin damar faɗaɗa harkokinsa domin samun kaso mai yawa a ɓangaren ta yadda zai ƙara shahara da harkar iskar gas,” in ji Dapo.

Nan da watan Nuwamba, ana sa ran NNPC zai kai jirage sama da biyu na gas zuwa kasuwannin ƙasashen Asiya, har da ƙari kafin ƙarshen shekara.

Tsarin kasuwancin ya ƙunshi masu kaya su kai tashoshin jiragen ruwan da ake kebe musu domin kayan da ake buƙata a kasunannin duniya.

Sai dai mai kayan ne ke ɗaukar alhalin inshorar kayansa har zuwa lokacin da za su isa inda ake buƙatarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here