NNPCL ta musanta zargin MURIC na yi wa matatar man Ɗangote maƙarƙashiya.
MURIC ta yi zargin cewa ƙarin kuɗin mai da NNPCL ya sanar a baya-bayan nan zai hana matatar Ɗangote sayar da man a farashi mai rahusa, sannan ta yi zargin cewa kamfanin NNPCL ne kawai zai riƙa sayen mai daga matatar.
To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Asabar, ya musanta zargin, yana mai cewa kasuwa ce ke ƙayyade farashin man kowace matata ciki kuwa har da ta Dangote.
”Ƙarin kuɗin mai da aka samu a baya-bayan nan ba zai hana matatar Dangote ko duk wata matata a cikin ƙasar nan samun ciniki ba. Idan ma suna ganin kamar kuɗin ya yi yawa, to matatar ta samu damar da za ta rage farashi domin samun ciniki a kasuwa”, in ji sanarwar.
Haka kuma NNPCL ɗin ya ce babu tabbacin samun ragin rafashi kan man da aka tace a gida fiye da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, kamar yadda matatar Dangoten ta tabbatar masa.
KU KUMA KARANTA:Man Fetur ɗin Ɗangote zai shiga kasuwa a makon gobe – NNPCL
Kamfanin NNPCL, ya ƙara da cewa zai sayi man Dangote ne kawai idan farashin man a kasuwar duniya ya fi yadda ake sayar da shi a Najeriya, don haka matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na da damar sayar da man ga duk wanda ke buƙata a kan farashin da suka daidaita.
”NNPCL ba shi da niyyar kankane sayar da man shi kaɗai a fagen kasuwancin da kowa ke da damar shiga a dama da shi, don haka maganar a ce NNPCL ne zai sayi mai daga matatar ba ta taso ba,” in ji sanarwa.
Kamfanin ya kuma ce babu ta yadda zai yi maƙarƙashiya ga kasuwancin da ya zuba hannun jarin biliyoyin daloli a cikinsa.