NNPC ta ba da tabbacin samar da wutar lantarki mai ƙarfin Megawat 52 a Maiduguri
Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur da Iskar Gas, Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo, ya yaba wa kamfanin NNPCL bisa nasarar aiwatar da manufofin Shugaban ƙasa ta hanyar samar da ayyuka masu tasiri ga ‘yan ƙasa.
Ɗaya daga cikin ire-iren ayyukan shine samar da Cibiyar Wutar lantarki ta Gaggawa a Maiduguri (MEPP), wadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙaddamar don amfanar ƴan kasa.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido ofishin cibiyar, a ranar Asabar, 14 ga watan Disamba.
Cikin waɗanda suka halarci ziyarar akwai; Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da Shugaban NNPCL, Mele Kyari da sauran manyan jami’an NNPCL.
KU KUMA KARANTA: Najeriya za ta samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt dubu ; Ministan Lantarki
Ita dai cibiyar samar da lantarki ta MEPP, wani aikin haɗakar wutar lantarki aka samar, mai karfin megawat 50, wanda aka ƙaddamar a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2023.
Rahotonni sun bayyana cewa tuni aka kammala aikin megawat 32 na aikin wanda a yanzu haka ya fara aiki, yayin da sauran megawat 18 zai fara aiki a shekarar 2025.