NJC ta dakatar da Alƙalan manyan kotuna a Anambra da Ribas
Majalisar kula da harkokin shari’a ta Najeriya (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a G.C Aguma na babbar kotun jihar Ribas da Mai Shari’a A.O Nwabunike na babbar kotun jihar Anambra daga gudanar da harkokin shari’a.
An dakatar da alƙalan 2 ne tsawon shekara guda ba tare da albashi ba sannan za a ci gaba da sanya idanu a kansu tsawon shekaru 2 a nan gaba.
A cewar sanarwar da NJC din ta fitar a ranar Juma’a, an ɗauki wannan mataki ne yayin karo na 107 na taron majalisar da babban jojin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jagoranta tsakanin ranakun 13 da 14 ga watan Nuwambar da muke ciki.
KU KUMA KARANTA:Hukumar Shari’a ta dakatar da Alkali kan yanke hukunci ta hanyar da ba ta dace ba
Jumlar alkalai 5 aka hukunta saboda aikata laifuffuka daban-daban.
Haka kuma majalisar ta bada shawarar yiwa wasu alkalan 2 ritayar dole saboda shigar da bayanan karya game da shekarunsu na haihuwa.
An bada shawarar yiwa alkalan 2 da suka hada alkalin alkalan jihar Imo, Mai Shari’a T.E Chukwuemeka Chikeka da girandi kadin jihar Yobe, Kadi Babagana Mahdi, ritayar dole saboda samunsu da yin karya game da shekarunsu.