‘Ni ban ga wanda zai iya gyara Nijeriya ba’ – Joe Igbokwe

0
1381
‘Ni ban ga wanda zai iya gyara Nijeriya ba’ - Joe Igbokwe

‘Ni ban ga wanda zai iya gyara Nijeriya ba’ – Joe Igbokwe

Joe Igbokwe, shahararren mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, ya koka kan yanayin da ƙasa ke ciki, inda ya ce har yanzu ba a haifi waɗanda za su gyara Najeriya ba.

Igbokwe, ɗaya daga cikin waɗanda suka yi wa Tinubu kamfen sosai wajen tunkarar zaɓen 2023, ya bayyana haka ne yayin da ya ke tsokaci kan tsadar rayuwa.

A wani saƙo da ya wallafa a Facebook a jiya Juma’a, Igbokwe ya koka da cewa yanzu buhun shinkafa ya kai sama da Naira 100,000.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya bai wa jihohi Naira biliyan 108 don magance ambaliya da radadin rayuwa – Shettima

“Duk da kamfanonin sarrafa shinkafa da muke da su a Najeriya, matata ta gaya min cewa buhun shinkafa yanzu ya kai sama da ₦100,000. Ba tare da kausasa harshe ba, ina ganin cewa maza da mata da za su ceto kasar nan daga kuncin rayuwa da hawaye ba a haife su ba tukuna,” ya rubuta.

Kwanan nan, Igbokwe, wanda ya yi aiki a kusan kowanne gwamnan Legas tun daga 1999, ya yi ta sukar wasu manufofin gwamnatin Tinubu, wanda ke nuni da ficewa daga abin da ya tsaya a kai.

Ko a makwanni biyu da suka gabata, ya koka kan karin kudin wutar lantarki, inda ya nemi Tinubu ya duba lamarin.

Leave a Reply