Firai Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya amince da sabon zagayen tattaunawa game da tsagaita buɗe wuta a Gaza, wanda ya gudana a biranen Doha da Alqahira, a cewar sanarwar da ofishinsa ya fitar a yau Juma’a, kwanaki bayan da ake ganin kamar tattaunawar ta cije.
Tun bayan da kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya zartar da ƙudirin neman a gaggauta tsagaita wuta a Gaza a Litinin ɗin da ta gabata, Isra”ila da ƙungiyar Hamas ke zargin juna da gazawa wajen cimma yarjejeniyar.
A Talatar da ta gabata, mai shiga tsakani ƙasar Qatar ta ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Hamas da Isra’ila akan tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da ake garkuwa dasu, sai dai dukkanin ɓangarorin dake rikici da juna da mai shiga tsakanin ba su yi ƙarin haske game da lamarin ba.
KU KUMA KARANTA:Kotun ICJ ta umarci Isra’ila da ta ɗauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza
Ofishin Netanyahu ya ce firimiyansa ya zanta da shugaban hukumar leƙen asirin Isra’ila, Mossad, David Damea game da tattaunawar sulhun, sai dai ba’a bayyana ko bamai ba, din zai yi balaguro zuwa biranen Doha da Alqahira domin halartar tattaunawar ba.
Yaƙi ya ɓarke tun bayan da Hamas ta ƙaddamar da wani hari da ba’a taɓa ganin irinsa ba, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka 1,160, galibinsu farar hula, a cewar ƙididdigarsu gwamnatin Isra’ila da kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
A cewar ma’aikatar lafiya dake ƙarƙashin gudanarwar ƙungiyar Hamas, Isra’ila ta ƙaddamar da harin ramuwar gayyar akan Hamas wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka mazauna yankin Gaza dubu 32 da 623 galibinsu mata da ƙananan yara.
Falasɗinawa masu fafutuka da makamai sun yi garkuwa da Yahudawa da baƙi ‘yan ƙasashen ketare 250 a yayin harin da aka kaiwa isra’ila na ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, sai dai an saki da dama yayin tsagaita wutar mako guda da aka yi a watan Nuwambar da ya gabata.
Isra’ila ta haƙiƙance cewar akwai sauran kimanin mutane 130 da ake garkuwa dasu a Gaza, ciki har da mutum 33 da ake zaton sun mutu; sojoji 8 da farar hula 25.