NDLEA a Legas ta kama miyagun ƙwayoyi na naira biliyan 16

0
16
NDLEA a Legas ta kama miyagun ƙwayoyi na naira biliyan 16

NDLEA a Legas ta kama miyagun ƙwayoyi na naira biliyan 16

Jami’an hukumar NDLEA da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi sun yi nasarar kama ƙwayoyi na fiye da naira biliyan 14 a ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa jami’an nata sun kama ƙwayoyin tapentadol guda miliyan 25, wadda ƙwaya ce da ta ninka tramadol ƙarfi sau uku.

Haka kuma hukumar ta ce ta kama kwalaben kodin 350,000 a tashar ruwa ta Tincan da ke Legas.

NDLEA ɗin ta ce ƙwayoyin na tapentadol miliyan 25 kuɗinsu ya kai kimanin naira biliyan sha uku da miliyan ɗari bakwai da ashirin da biyar (N13,725,000,000.00).

Haka kuma kuɗin kodin ɗin ya kai naira biliyan biyu da miliyan ɗari huɗu da hamsin (N2,450,000,000.00), wanda idan aka yi jimlar waɗannan kuɗi sun kai naira biliyan sha shida da miliyan ɗari da saba’in da biyar (N16,175,000,000).

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta shirya taron ƙarawa juna sani ga ɗaliban kiwon lafiya a Katsina

Hukumar ta NDLEA ta ce ƙwayoyin na tapentadol an gano su ne a cikin katan 500 a cikin wasu kwantenoni a ranar Talata 17 ga Satumba, inda kuma wata kwantenar wadda aka bincika a ranar aka ganta da kwalabe 175,000 na maganin tari mai ɗauke da kodin a cikin katan 875.

Sannan sai kwantena ta uku ita ma aka ga kwalaben kodin 175,000 ɗauke da kodin ɗin wadda ita kuma aka gano ta a ranar 20 ga Satumba.

Ana yawan samun rahotannin safarar miyagun ƙwayoyi a Nijeriya inda akasarinsu ake shigar da su ƙasar daga wasu ƙasashen waje.

Sai dai hukumar ta NDLEA ta sha jaddada cewa tana iya bakin ƙoƙarinta domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyin.

Leave a Reply