Nasarorin da aka samu a jihar Katsina – ‘Yansanda
Daga Idris Umar, Zariya
A cikin wannan satin Kakakin Rundunar ‘yansandar Jihar Katsina, DSP Sadiq Abubakar, ya gabatar da taƙaitaccen bayani ga manema labarai a hedkwatar ‘yansanda ta jihar, dangane da nasarorin da aka samu a yakin da ake yi da aikata laifuka a jihar.
A ranar 13 ga watan Janairu, 2025, jami’an rundunar sun kama mutane biyu da ake zargi da sacewa da kuma kashe wani yaro mai shekaru 12, a garin Dankama, ƙaramar hukumar Kaita.
An bayyana cewa yaron ya ɓace a ranar 11 ga watan Janairu, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wani shagon magani.
Masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa naira miliyan 25, amma daga bisani suka kashe yaron duk da ƙoƙarin iyalansa na yin sulhu.
Bayan bincike, an kama masu laifin guda biyu, Mutaka Garba da Yusuf Usman, waɗanda suka amsa laifinsu.
A ranar 31 ga watan Disamba, 2024, rundunar ta kama wasu gungun mutane da ake zargi da haɗa kuɗaɗen bogi da sayarwa.
KU KUMA KARANTA: ;’Yansanda sun gurfanar da Shamsiyya a kotu bisa zargin satar wayoyi a Kano
An kama mutum ɗaya mai suna Aliyu Isa dauke da takardun kudaden bogi rafa biyu na dala $100 yayin da yake ƙoƙarin musanya su da naira 300,000. Wannan ya kai ga gano sauran ‘yan Damfara tare da ƙwace takardun kuɗaɗen bogi guda 1,018.
A ranar 11 ga watan Janairu, 2025, an kama wani mutum mai suna Abdullahi Ali mai shekaru 51, wanda aka samu yana lalata wasu motoci a harabar asibitin koyarwa na Katsina. Ana zargin ya sace hula guda hudu da kuma naira 650,000 daga cikin wata mota mallakar dan majalisa Hon. Zaharadeen Usman.
A watan Janairu 2025, jami’an rundunar sun yi nasarar kai samame a wasu wurare a cikin jihar Katsina da karamar hukumar Funtua, inda aka kama mutane 15 da ake zargi da aikata laifuka kamar fashi da makami da sauran aikata laifuka.
An ƙwace muggan makamai, miyagun ƙwayoyi da wasu kayayyaki daga hannunsu.
A ranar 30 ga watan Disamba, 2024, rundunar ta kama wani ɗan bijilante mai suna Ismail Isa dauke da Kwafsan Alburusai na bindigogi AK47 guda 15 a kan hanyar Funtua. Ana zargin ya same su ne ba bisa ka’ida ba kuma yana kan hanyarsa ta zuwa garin Shuaki domin sayar da su ga wani mutum da ke gudun hijira.
Rundunar ta kuma bayyana nasarar kama wasu gungun mutane huɗu da suka kware wajen sauya katunan SIM na jama’a don zambar kuɗaɗe daga asusun bankinsu.
An kwato katunan SIM guda 32 daga hannun wadanda ake zargi, ciki har da wani ma’aikacin banki.
DSP Sadiq Abubakar ya bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama za su gurfana gaban kotu da zarar an kammala bincike, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da tsaro a jihar Katsina.