Nan da shekarar 2035 za a kawar da cutar tarin fuka a Najeriya – Remi Tinubu
Ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da take jawabi a gangamin Najeriya na yaƙi da tarin fuka na 2024 da ya gudana a Abuja.
Uwargidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu, ta bayyana fatan ganin Najeriya ta kawar da cutar tarin fuka kan nan da shekarar 2035, inda ta jaddada mahimmanci yin hadin gwiwa da kirkirar dabarun dakile yaduwar cutar a kasar.
Ta kara da cewa duk da munin alkaluman yaki da cutar tarin fuka a Najeriya an samu cigaba a bangaren ganowa da maganceta, inda ta alakanta hakan ga jajircewar gwamnatin tarayya da hukumomin bada agaji irinsu usaid da Global Fund.
KU KUMA KARANTA:Ƙofofin ECOWAS a buɗe suke ga ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso – Tinubu
Ta bayyana hakan ne a jiya Talata yayin da take jawabi a gangamin Najeriya na yaki da tarin fuka na 2024 daya gudana a Abuja.
Uwargidan shugaban kasar ta yabawa masu ruwa da tsaki game da kokarinsu saidai ta bukaci su ci gaba da jajircewa domin cimma muradan da duniya ta sanya a gaba na kawar da tarin fuka.
Haka kuma ta jaddada mahimmancin gangamin a matsayin wani dandali na musayar ilmi da bunkasa dabaru tare da sabunta aniyar yaki da tarin fuka.