Nan da shekarar 2030 rabin ayyuka za su koma kan na’urorin zamani – Masana

0
84

A cewar masanin, lokaci ya yi da matasa za su ƙara mayar da hankalinsu kan koyon ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa wanda hakan zai ba su dama su yi aiki daga ko’ina a duniya.

Ƙwararre a ilimin kimiyya da fasaha a Najeriya, Dakta Grema Kyari ya ce nan da shekara ta 2030 rabin ayyukan duniya za su koma kan na’urori, wanda hakan zai rage dogaro ga aikin ƙarfi.

Kyari ya ce hakan a lokaci guda na nuna damar samun ayyuka cikin sauƙi bisa ƙwarewa a fannin fasaha.

Ya ƙara da cewa wannan farkarwa ne ga waɗanda ke kammala makaranta da ƙorafin ba ayyukan yi su dage wajen koyon fasahar sana’a da ke kan na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Kyari ya ce daga ko’ina mutum ya ke rayuwa zai iya samun aikin yi da zai ba shi albashi ko kuɗin shiga don kula da tsadar rayuwa.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

Kalaman na Kyari na zuwa ne yayin da wata tawagar ƙwararru suka zaga sassan Najeriya musamman yankunan karkarar arewa don wayar da kan matasa kan wannan abun da ke tunkarowa nan da shekaru 6 masu zuwa.

Shi kuma babban sakatare a ma’aikatar kasuwanci da masana’antu Ambasada Nura Abba Rimi ya ce ‘yan Najeriya na ci gaba da samun ƙwararru da kan yi fice a duniya kuma gwamnati na ba su ƙwarin gwiwa.

Ƙarancin wutar lantarki, rashin wayar da kai da tsadar kayan aiki na daga cikin dalilan da kan kawo rashin amfanar ɗalibai da ma sauran ‘yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi wajen cin moriyar fasahar zamani a cewar ƙwararru.

Leave a Reply