Najeriya za ta kwashe ‘yan ƙasarta daga Lebanon
Gwamnatin Najeriya ta ce saboda taɓarɓarewar tsaro a gabas ta tsakiya, musamman faɗan da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas za ta kwashe ‘yan ƙasar da ke Lebanon.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Ambasada Eche Abu-Obe, ya ce dama ƙasar ta kwashe ‘yan Najeriya da ke kudancin Lebanon zuwa babban birnin ƙasar Beirut.
KU KUMA KARANTA:Najeriya ta fara shirin kwaso ‘yan ƙasarta daga Lebanon
“Tun a watan Agusta ofishin jakadancin Najeriya a Lebanon ke fitar da takardar gargaɗi da ba da shawara ga ‘yan ƙasar kan batun yadda za su bar Lebanon ta hanyar jiragen fasinja da suke zuwa ƙasar.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “ya zuwa yau dai babu wani ɗan Najeriya da ya rasa ransa tun bayan ɓarkewar faɗan.”
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta tabbatar da cewa gwamnatin ƙasar na aiki da masu ruwa da tsaki don ganin an kare rayuwar ‘yan ƙasar a Lebanon har zuwa lokacin da za’a kwaso su zuwa gida Najeriya.