Najeriya za ta ba da lasisin haƙar ma’adinai ga kamfanonin da ke aiki cikin ƙasar

0
112

Najeriya za ta ba da sabbin lasisin haƙar ma’adinai ne kawai ga kamfanonin da suka gabatar da wani shiri kan yadda za a sarrafa ma’adanai a cikin gida, ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin da ake samar da su, kamar yadda kakakin gwamnati ya tabbatar a ranar Alhamis.

Wannan na nuni da cewa an samu sauyi daga tsarin da Najeriya ta kwashe shekaru da dama ta yi na fitar da albarkatun ƙasa zuwa ƙasashen waje yayin da gwamnatocin ƙasashen Afirka ke ɗaukar matakai na fitar da ƙarin ƙimar ma’adinan da suke da shi.

Domin ƙarfafa zuba jari, Najeriya za ta baiwa masu zuba jari ƙwarin guiwa da suka haɗa da hana harajin shigo da kayan aikin haƙar ma’adanai, da sauƙaƙa samun lasin na samar da wutar lantarki, da ba da damar mayar da cikakkiyar ribar da aka samu da kuma inganta tsaro, in ji Segun Tomori, mai magana da yawun ministan bunƙasa ma’adanai na Najeriya.

Tomori ya ce, “Kafin musanya, dole ne mu sake duba shirinsu na kafa masana’antar da kuma yadda za su ƙara wa tattalin arziƙin Najeriya daraja.” Bai bayyana lokacin da za a kammala ƙa’idojin ko kuma za su fara aiki ba.

Sai dai a makon da ya gabata Ministan Ma’adanai Dele Alake, ya ce a yanzu manufar gwamnati ce ta sanya ƙarin darajar ya zama sharaɗin samun lasisi ta yadda za a samar da ayyukan yi da kuma taimakawa al’ummomin yankin.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kaduna zai ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Kuriga

Alake, wanda kuma ke jagorantar wata ƙungiyar dabarun haƙar ma’adinai ta Afirka da ta ƙunshi ministocin ma’adinai daga Uganda, Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, Saliyo, Somalia, Sudan ta Kudu, Botswana, Zambiya da Namibiya, na da ƙudirin yin wani yunƙurin a duk faɗin nahiyar don samun mafi girman fa’ida daga cikin gida daga binciken ma’adinai.

Najeriya, wacce ke kan gaba wajen samar da makamashi a nahiyar Afirka, ta yi ta faman fitar da kimarta daga ɗimbim albarkatun ma’adinai da take da su, sakamakon rashin kuzari da kuma rashin kulawa. Ɓangaren haƙar ma’adinai da ba a ci gaba ba yana ba da gudummawar ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari na dukiyoyin cikin gida na ƙasar.

A shekarar da ta gabata Najeriya ta fitar da ma’adinan dala da yawansu ya kai kimanin Naira biliyan 137.59 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 108.34, musamman zuwa ƙasashen China da Malaysia, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta bayyana.

Gwamnati na da burin ƙara zuba jari a fannin ta hanyar ba da wasu lasisi, inda ta kafa wani kamfani mai fa’ida na ma’adinai mallakin gwamnati wanda ke baiwa masu zuba jari kashi 75% na hannun jari tare da kafa wani sashin tsaro na musamman da ke da alhakin yaƙi da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply