Najeriya tana son sayen jiragen yaƙi da helikwaftoci don ƙarfafa yaƙi da ta’addanci
Rundunar sojin sama tana neman samun jiragen yaƙi samfurin M-346 da Italiya ta ƙera guda 24 da kuma jirage masu sauƙar ungulu na AW-109 Trekker a wani ɓangare na shirin sabunta jiragen yaƙinta, in ji mai magana da yawun rundunar a ranar Litinin.
Mai magana da yawun rundunar sojin sama, Olusola Akinboyewa, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, tawagar ƙarƙashin jagorancin shugaban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Hasan Abubakar, ta gana da shugabannin kamfanin ƙera jiragen na Italiya Leonardo S.p.A. a birnin Rome wanda ya tabbatar da cewa ana sa ran kai jirgin M-346 guda uku na farko a farkon shekarar 2025, tare da isar sauran a tsakiyar 2026.
Ana sa ran karɓar jirage masu sauƙar ungulu na Trekker nan da farkon 2026, in ji Akinboyewa.
“Sayen M-346 da Trekker muhimman matakai ne na sabunta jiragen yaƙi,” in ji Abubakar yana mai jaddada bukatar samar da cibiyar gyaransu a Najeriya don ba da tallafi na dogon lokaci, musamman ga jiragen yaƙin na M-346.
Najeriya dai ta ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa a fannin soji a shekarun baya-bayan nan a ƙokarinta na daƙile hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar da kuma yaƙin shekaru 15 na ƙungiyar Boko Haram da ƙungiyar Daesh da ake ƙira ISWAP a yankin arewa maso gabas.
A farkon wannan shekarar, ƙasar da ke yammacin Afirka ta karɓi sabbin jiragen sama guda biyar, waɗanda suka haɗa da jirage masu sauƙar ungulu na TA T129 ATAK guda biyu da aka ƙera a Turkiyya.
A watan Yuni, Najeriya ta karɓi jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu “Huey” guda biyu, baya ga Trekkers guda biyu da ta riga ta samu, da kuma jiragen yaƙi 12 na Amurka A-29 Super Tucano da ta samu a shekarar 2021 domin yakar masu tada ƙayar baya.
Tana da jirage don isar da jirage marasa matuƙi na Wing Loong II na China.