Najeriya ta soki Amurka kan gargaɗin cewa otel-otel na ƙasar na fuskantar barazanar tsaro

0
198

Najeriya ta caccaki Amurka kan shawarwarin da ta bayar cewa otel-otel ɗin ƙasar na fuskantar barazanar tsaro.

Gargaɗin na Amurka zai iya jawo “fargaba ba gaira ba dalili” tare da yi wa tattalin arziki illa, a cewar Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris.

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da wani gargaɗi a ranar Juma’a da ke cewa “manya-manyan otel-otel a manyan biranen ƙasar na fuskantar barazanar tsaro,” amma ya ce hukumomin tsaron ƙasar na aiki tuƙuru don magance waɗannan barazana.

“Waɗannan shawarwari ba sa kawo komai idan ba tayar da fargaba ba, kuma za su iya yin mummunan tasiri a kan tattalin arziki, ba a ma maganar tasirinsu na daƙushe ƙoƙarin gwamnati na jawo hankalin masu zuba jari,” kamar yadda Minista Idris ya shaida wa taron manema labarai a ranar Litinin.

KU KUMA KARANTA: <em>Shawarwari 15 da ƴan sanda suka bayar don kare kai a Najeriya</em>

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin tana ci gaba da bai wa tsaron ƴan ƙasa da sauran baƙin da ke shiga cikinta muhimmanci, ta hanyar “ɗaukar ƙwararan matakai.”

A bara, Amurka ta fitar da irin wannan gargaɗin tana mai shawartar Amurka da su guji yin tafiye-tafiye zuwa jihohin Najeriya da dama saboda “barazanar ta’addanci.

Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta a kan hakan, kuma a hankali Amurka ta janye gargaɗin tsaron.

Ƙwararru sun kuma dasa ayar tambaya a kan irin waɗannan shawarwari da Amurka ke bayarwa a kan ƙasashe a faɗin duniya.

Dakarun tsaron Najeriya suna ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsaro da ake fama da su na ƙungiyar Boko Haram da gungun masu satar mutane don kuɗin fansa a ƙasar.

Leave a Reply