Najeriya ta sha da ƙyar a hannun Canada

0
280

Daga Ibraheem El-Tafseer

Najeriya ta sha da ƙyar a hannun Canada bayan da mai tsaron gida ta Najeriyar Chiamaka Nnadozie ta damƙe bugun fanareti a minti na 50 bayan fara wasa.

Kyaftin ɗin Canada, Christine Sinclair, wadda ta buga fanaretin na neman kafa tarihin zama wadda ta zura ƙwallo a gasar ƙwallon ƙafa ta mata guda shida.

Ɗaya daga cikin ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta a wasan shi ne katin kora da aka bai wa ‘yar wasa Deborah Abiodun.

Amma duk da haka Najeriya ta tsira da maki ɗaya a wasan, yayin da ita ma Canada ta tsira da maki ɗaya a rukunin B, yayin da mai masauƙin baƙi Australia ke jagorantar rukunin da maki uku.

Leave a Reply