Najeriya ta mai da martani bayan sabon zargin yi wa Nijar maƙarƙashiya

0
30
Najeriya ta mai da martani bayan sabon zargin yi wa Nijar maƙarƙashiya

Najeriya ta mai da martani bayan sabon zargin yi wa Nijar maƙarƙashiya

Sabbin zarge-zargen suna nuni da cewa Faransa za ta samar da kuɗin maƙarƙashiya hamɓarar da gwamnatin soja a Nijar ko tilasta ta ta sake hamɓarerren shugaba Muhammad Bazoum.

Gwamnatin Najeriya ta sake fitowa ta yi watsi da sabbin zarge-zarge na neman hargitsa Jamhuriyar Nijar ta hanyar amfani da ‘yan ta’adda.

Sabbin zarge-zargen suna nuni da cewa Faransa za ta samar da kudin makarkashiyar hambarar da gwamnatin soja a Nijar ko tilasata ta ta sake hambarerren shugaba Muhammad Bazoum.

KU KUMA KARANTA:2025: Mu haɗa kai mu ci gaba da tafiya domin gina ƙasar nan – Shugaba Tinubu

Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan zargin ke fitowa ba. Idan ba a manta ba, a watan Disambar da ta gabata, shugaban gwamnatin sojan Nijar Birgediya Janar Abdulrahman Tchiani ya ce shugaba Tinubu na biyewa Faransa wajen karfafa ‘yan ta’addan Lakurawa don wargaza zaman lafiyar Nijar.

Zargin ya nuna cewa har an yi taro da ‘yan Boko Haram a yankin jihar Borno da dumbula mu su makamai; sai dai kuma gwamnatin Najeriya ta nesanta kan ta daga yi wa Nijar makirci.

Wakilin Muryar AMurka Nasiru Adamu El-Hikaya, ya ruwaito cewa mai taimakawa shugaba Tinubu a fannin labaru Abdul’aziz Abdul’aziz, ya ce “gaskiya mu har yanzu mu na cike da mamaki ne ganin yadda wasu jami’an gwamnatin sojan Nijar suke neman saka Najeriya cikin matsalolin cikin gida da su ke fama da su.”

A tattaunawar shi da wakilin namu, jagoran malaman da su ka shiga tsakani wajen kawar da barazanar matakan sojin ECOWAS kan Nijar Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci a yi takatsantsan “Najeriya da Nijar tamkar Danjuma ne da Danjummai in ta kama za mu sake sa baki don sulhu alheri ne.”

Leave a Reply