Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki – CNG

0
57
Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki - CNG

 

Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari saboda wahalhalun tattalin arziki – CNG

Gamayyar ƙungiyoyin arewacin Najeriya, CNG,
ta ce ba a taɓa samun gwamantin da aka sami koma-baya ba a Najeriya, kamar mulkin Bola Ahmed Tinubu ba.

A cewar CNG, maimakon a samu ci gaba sai ma koma-baya a ake ta samu, saboda manufofin da gwamantin ta ke futo da su babu wanda zai ce tana jin ƙasan talakan ƙasar.

Kwamared Jamilu Aliyu Chiranci shi ne shugaban ƙungiyar ta CNG, ya shaida wa BBC cewar Najeriya na tunkarar wani mataki mai haɗari, saboda wahalhalun tattalin arziki, da hauhawar farashi, da talauci da ya yi wa ƴan ƙasar katutu

KU KUMA KARANTA:Da ba a cire tallafin mai ba, da wahalar da za’a sha a Najeriya ta fi ta yanzu – Gwamnatin tarayya

Ya ce dole CNG ta sa daukar wannan mataki sakamakon yadda ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa musaman tashin farashin kayayyaki a ɗaukacin faɗin ƙasar.

Gamayar ƙungiyoyin arewacin ta Najeriya ta ce, lamarin ƙangin da ake fama da shi a ƙasar ya fi ƙamari a yankin arewacin ƙasar, saboda yanayin da al’ummar yankin ke ciki.

Duk abinda shugaban ƙasa zai yi, akwai buƙatar ya tsaya ya mayar da hankali kan ceto ƙasar nan, wanda ina da yaƙinin cewar bazai so a ce a lokacin sa Najeriya ta shiga yanayin da ƴan ƙasar za su yi mata turjiya ba”

Sannan ya ce ’mutam miliyan 133 a Najeriya na fama da talauci, sannan mutane miliyan 20 ba su da aikin yi ko ma a ce ba su da isasshen aiki”, In ji Kwamrated Chiranci.

Da hakane CNG ɗin ta bai wa shugaban ƙasar Ahmed Bola Tinubu wa’adin mako guda da ya hanzarta tare da yin nazari game da halin da al’ummar ƙasar ke ciki, tare da ɗaukar matakan gaggawa da za su kawo wa ƴan Najeriyar sauƙin rayuwa.

Leave a Reply