Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziƙi

‘Yan Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin yanayi mafi muni na taɓarɓarewar tattalin arziƙi a ƙasar ta Yammacin Afirka a cikin shekaru da dama sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Hauhawar farashin ya faru ne sakamakon manufofin kuɗi da ya sa darajar kuɗin ƙasar ya faɗi warwas idan aka kwatanta da dalar Amurka. Lamarin dai ya haifar da fushi da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Alƙaluman gwamnati na baya-bayan nan da aka fitar a ranar Alhamis, sun nuna hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairu ya ƙaru zuwa kashi 29.9 cikin 100, mafi girma tun shekarar 1996, galibi ya shafi abinci da abubuwan sha.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kuɗin Najeriya, Naira ta ƙara faɗuwa inda ake canjin dalar Amurka ɗaya akan Naira 1,524, lamarin da ke nuna asarar da aka samu da kashi 230 cikin 100 daga bara.

KU KUMA KARANTA:Taron ƙungiyar AU na nemo hanyar warware matsalolin da ke addabar nahiyar Afirka

“Iyalina yanzu suna rayuwa cikin dogaro ga Allah,” in ji wani ɗan kasuwa Idris Ahmed, wanda ke da wani kantin sayar da tufafi a Abuja babban birnin Najeriya, kuma cinikinsa ya ragu daga matsakaicin dala 46 a kullum zuwa dala 16.

Faɗuwar darajar kuɗin ta ƙara tsananta a halin da ake ciki na yanzu, kuma yana ƙara lalata kuɗaɗen shiga da kuma na tanadi. Lamarin ya danne miliyoyin ‘yan Najeriya waɗanda tuni ke kokawa da wahalhalu saboda sauye-sauyen da gwamnati ta yi ciki har da cire tallafin man fetur wanda ya janyo farashin man ya ninka sau uku.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *