Naira na daga cikin takardun kuɗi mafi rashin daraja a Afrika – Bankin Duniya

0
33
Naira na daga cikin takardun kuɗi mafi rashin daraja a Afrika - Bankin Duniya

Naira na daga cikin takardun kuɗi mafi rashin daraja a Afrika – Bankin Duniya

Takardar naira na daga cikin takardun kuɗi mafi rashin daraja a nahiyar Afrika a cikin shekarar 2024.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wani sabon rahoto a kan kuɗaɗen nahiyar Afrika da bankin duniya ya fitar.

Rahoton na bankin duniya ya nuna cewa Naira ta yi faɗuwar baƙar tasa da ya mayar da darajar ta bayan ta takardar kuɗin Birr na ƙasar Ethiopia da Sudanese Pound na ƙasar Sudan ta Kudu.

A cewar rahoton, darajar takardar Naira na cigaba da faɗuwa saboda ƙaruwar neman Dalar Amurka da kuma ƙarancin kwararowar Dalar Amurka cikin Najeriya a watannin baya bayan nan.

KU KUMA KARANTA: Za a ƙara kuɗin shiga jirgin ƙasan na Abuja zuwa Kaduna

Takardar naira ta rasa darajar ta da kaso 43% ya zuwa watan Agusta na shekarar 2024, kamar yadda rahoton ya nuna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa darajar Naira ta sake faɗuwa zuwa ₦1,700 kowacce Dalar Amurka ɗaya a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024, a kasuwar canjin kuɗi.

Hakan ya nuna cewa darajar naira ta sake faɗuwa da 0.29% daga ranar 11 ga watan Oktoba da ake canjin Dala ɗaya a kan N1,695.

Abin mamakin shine yadda darajar naira ke cigaba da faɗuwa duk da tashin farashin gangar man fetur a kasuwar duniya.

Leave a Reply