Connect with us

NAHCON

NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu

Published

on

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce ƙasar Saudiyya ta ba maniyyatan ƙasar nan da mako uku su fara biyan kafin alƙalami na kuɗaɗen kujerar aikin hajjin shekara ta 2024.

A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce Saudiyya ta ajiye ranar 4 ga watan Nuwamba domin kammala shirye-shiryen da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar.

Ta ce bayan nan ne hukumar za ta tantance ainihin yawan maniyyatan wanda daga nan ne za ta tattauna batun farashin kujera, har kuma ta yanke shi daga ƙarshe.

Fatima ta kuma ce shirye-shiryen da hukumar ta fara yi ne suka sa a yayin tattaunawar shugabannin Hukumomin Alhazai na jihohin Najeriya a kwanakin baya ta sanar da Naira miliyan huɗu da rabi a matsayin kuɗin kujera a hajjin baɗi.

KU KUMA KARANTA: An bayyana kuɗin da maniyyata aikin hajjin 2024 za su ajiye a Kano

Sanarwar ta ce, “Da farko dai dalilai uku ne suka sa za a fara ajiye waɗannan kuɗaɗen na kafin alƙalami. Na farko shi ne saboda jihohi su san yawan alhazan da za su biya kuɗin, aƙalla kafin nan da ranar 4 ga watan Nuwamba, wanda shi ne lokacin da Saudiya ta sanya domin kammala shirye-shiryen dukkan masu ruwa da tsaki.

“Yin hakan zai taimaka wa hukumomin yin dukkan tsare-tsaren da suka kamata a kan lokaci.”

Sai dai ta ce an amince daga bisani za a ba maniyyatan dama su cika ragowar kuɗaɗen sannu a hankali zuwa lokacin da za a sanar da ainihin farashin kujerar.

Ta kuma ce duk waɗanda suka gaza biyan adadin da aka fara ƙayyadewa, to su kuka da kansu idan aka ƙirga yawan maniyyatan babu sunansu.

Sai dai ta tsaya kai da fata cewa har zuwa wannan lokacin, akwai yiwuwar mafi ƙarancin farashin kujerar a baɗi ya kai naira miliyan huɗu da rabi, kamar yadda hukumar ta sanar a kwanakin baya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Hukumar Alhazan Nijeriya ta ƙaryata zargin bai wa mahajjata abinci kaɗan

Published

on

Hukumar Alhazan Nijeriya ta ƙaryata zargin bai wa mahajjata abinci kaɗan

Hukumar Alhazan Nijeriya ta ƙaryata zargin bai wa mahajjata abinci kaɗan

Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ƙaryata wani labari da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta da ake zarginta da bai wa mahajjata abinci ɗan kaɗan.

A ranar Talata ne aka fara yaɗa hoton nau’in abincin karin kumallo da ke nuna kunu kaɗan a wani mazubi da kuma ƙosai ƙwaya uku, inda aka ce wani ɗan jarida ne ya fara yaɗawa don nuna wa duniya yadda ake “bai wa mahajjata abinci kaɗan bayan biyan naira miliyan takwas kuɗin kujerar ajji.”

Lamarin ya jawo Allah wadai a shafukan intanet a Nijeriya, inda aka dinga zargin hukumar da “son wulaƙanta alhazai” kan irin nau’in abincin da take ba su duk da makuɗan kuɗaɗen da suka biya.

Sai dai a sanarwar da ta fitar a ranar Talata da marece mai ɗauke da sa hannun Hajiya Fatima Sanda Usara, mai magana da yawun NAHCON, ta ce “an jawo hankalinmu kan wani labarin ƙarya da shafin Facebook na wani Babagana Digima ya wallafa, da ke nuna wani nau’in abinci da aka ce shi muke raba wa alhazan Nijeriya bayan da suka biya kuɗin kujerar Hajji har naira miliyan takwas.”

KU KUMA KARANTA: Rukunin farko na Alhazan Kano sun tashi zuwa Saudiyya

“Bayan yin abin da ya dace a kan labarin daga tushe mun yi imani cewa dokokin watsa labarai ba su yarda ɗan jarida da ya san abin da yake yi ya dogara da labari daga Facebook kaɗai ba.

Wani abin takaici shi ne cewa ɗan jaridar da ya ɗauki labarin daga Facebook yana nan a Nijeriya bai je Saudiyyan ba,” in ji sanarwar.

NAHCON ta ce da samun labarin ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai ta ja hankalin wanda ya fara ƙirƙirarsa a fili da a bayyane kan rashin sahihancin ikirarin nasa inda ta nemi ya janye zargin, tana mai yi masa uzurin ko bisa rashin sani ya wallafa, amma sai ya ƙi yin hakan.

“Duk da haka alhazai da dama da suke Makkah a halin yanzu sun yi ta ƙaryata zargin nasa ta hanyar wallafa hotunan ainihin abincin da ake ba su a ƙasan labarin da ya wallafa, sannan ma’aikatan NAHCON ma da suke can sun yi bayanin irin abincin da ake bayarwa, suna masu cewa hoton da ya saka din an yi masa kwaskwarima ne, kuma ƙarya ce tsagwaronta.

“Amma duk da haka gidan jaridar Sahara Reporters sun yi biris da hakan.

Kuma jaridar ta yi amfani ne kawai da wani hoto na mahajjatan Babban Birnin Tarayya na abin karyawar da aka ba su a otel ɗinsu a Makkah, amma sai aka yi masa kwaskwarima aka wallafa shi.

A ƙarshe hukumar Alhazan ta yi ƙira ga al’umma da su yi watsi da labarin ƙaryar da ake watsawa a kan batun abin karyawar tana mai nanata cewa ƙarya ce da son ɓata mata suna.

Continue Reading

Labarai

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajjin 2024

Published

on

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta ƙara farashin kujerar Aikin Hajjin bana da miliyan N1,918,032.91, inda ta bai wa maniyyata wa’adin zuwa 28 ga watan Maris ɗin 2024 su biya cikon kuɗin.

Mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi.

Hukumar ta NAHCON ta ce an samu wannan ƙarin ne sakamakon ƙaruwar farashin dala a Najeriya.

A baya dai NAHCON ta saka kuɗin Aikin Hajjin bana kan Naira miliyan 4.9, lamarin da ya sa aka yi ta kokawa da hakan.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta sanar da yadda Saudiyya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana

Sai dai a halin yanzu ana buƙatar waɗanda suka biya kafin alƙalamin na miliyan 4.9 su biya ƙarin miliyan 1.9, wanda hakan ya kai jumullar kuɗin kowane maniyyaci zuwa miliyan 6.8.

Haka kuma hukumar ta bai wa maniyyatan zuwa 28 ga watan Maris su biya wannan cikon.

Sai dai a wani ɓangaren kuma hukumar ta sanar da cewa duk wani sabon maniyyaci daga arewacin Najeriya wanda yake son biyan kuɗin kujera a yanzu zai biya N8, 254, 464.74.

Sai kuma sabbin maniyyata daga jihohin Adamawa da Borno za su biya N8,225, 464.74 sai kuma ƴan kudancin Najeriya za su biya N8, 454, 464.74.

Continue Reading

Labarai

NAHCON ta sanar da yadda Saudiyya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana

Published

on

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun yi ragin kuɗin Hajji ga maniyyatan da za su sauƙe farali a bana, 2024, domin farantawa mahajjata.

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar cewa shugabata, Jalal Ahmad Arabi, ne ya nemo ragin da aka yi, wanda ya shafin kuɗin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake wa alhazai a Saudiyya.

Mai magana da yawun hukumar NACHON, Fatima Sanda Usara ce ta sanar da hakan a ranar Laraba, inda ta ce a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kuɗin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina daga Riyal daga 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu

“Zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma an rage shi zuwa Riyal 5,393 zuwa 4,770,” in ji ta.

Sai dai duk da haka, sanarwar ba ta bayyana ko NAHCON za ta yi wa maniyyayatan Najeriya ragin kuɗin kujera daga naira miliyan 4.5 da ta sanar tun da farko ba.

Kazalika ana hasashen duk da sauƙin da wannan Saudiyya ta yi, da wuya maniyyayatan Najeriya su shaida sauƙin — daga naira miliyan 3 da suka biya a 2023 — sakamakon tashin farashin Dala.

Farashin kuɗaɗen ƙasashen waje musamman Dala sai ƙara ƙaruwa yake a Najeriya, lamarin da ke ƙara haifar da tsadar rayuwa a ƙasar.

Akasari ana biyan kuɗin aikin Hajji da sauran huldodin ƙasa da ƙasa, kamar aikin Hajji da sauransu ne da Dala ko sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.

Faɗuwar darajar kuɗin Najeriya, naira da tashin dala da danginsa a ƙasar ta sa a duk shekara kuɗin aikin Hajji ƙaruwa.

A sakamakon haka ne aka samu ƙarin kashi 50 a kuɗin aikin Hajjin 2024 a kan na 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu raguwar maniyyayatan Najeriya da za su sauƙe farali a bana a sakamakon tsadar kuɗin kujera.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like