Na gaji bashin Naira biliyan 8.9 a asusun APC bayan zama na shugaban jam’iyyar – Ganduje

0
29
Na gaji bashin Naira biliyan 8.9 a asusun APC bayan zama na shugaban jam'iyyar - Ganduje

Na gaji bashin Naira biliyan 8.9 a asusun APC bayan zama na shugaban jam’iyyar – Ganduje

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa kwamitin koli na jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin sa, ya gaji bashin Naira Naira biliyan 8.9.

Ganduje ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake magana a taron zartarwa na kasa na jam’iyyar APC.

KU KUMA KARANTA:APC na daf da karɓar jiga-jigan NNPP ciki har da ‘yan majalisa – Ganduje

A cewarsa, bashin ya taru ne sakamakon harkokin Shari’a kafin zaɓe da shari’o’in zabe, da kuma kararrakin zaben ‘yan majalisa, gwamna, da shugaban kasa.

Sai dai ya bayyana cewa Farfesa Abdul Kareem Kana (SAN), mai baiwa APC shawara kan shari’a na kasa, ya dukufa wajen ganin an rage bashin.

“Har yanzu muna kira ga kwamitin zartarwa na kasa da ya yi duba a kan haka,” in ji shi.

Leave a Reply