Mutum biliyan 1.1 na cikin matsanancin talauci a duniya – MƊD
Wani sabon rahoto na shirin raya ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce fiye da mutane biliyan daya ne ke fama da matsanancin talauci a faɗin duniya, inda yara suka fi yawa a cikin waɗanda abin ya shafa.
Rahoton wanda da aka sake a ranar Alhamis, da aka wallafa da haɗin gwiwar ƙungiyar Oxford Poverty da ta Human Development Initiative (OPHI) ya yi nuni da cewa, yawan talauci ya ninka sau uku a kasashen da ake yaƙi, yayin da shekarar 2023 ta kasance mafi yawan tashe-tashen hankula a duniya tun bayan yakin duniya na biyu.
UNDP da OPHI sun fitar da ma’aunin talauci da yawa a kowace shekara tun daga 2010, suna tattara bayanai daga ƙasashe 112 da ke da adadin mutum biliyan 6.3.
Rahoton yana la’akari da abubuwa kamar rashin isassun gidaje da tsaftar muhalli da wutar lantarki da makamashin girki da abinci mai gina jiki da zuwa makaranta.
Babban jami’in ƙididdiga na hukumar ta UNDP Yanchun Zhang ya ce, “Alƙaluman MPI na shekarar 2024 sun ba da bayani mai ban sha’awa: mutum biliyan 1.1 na fama da tsananin talauci, inda miliyan 455 ke rayuwa a cikin matsanancin rikici.”
Zhang ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa, ga matalautan ƙasashen da ke fama da rikici, gwagwarmayar neman bukatu na yau da kullun ya kasance mafi munin yanayi.
KU KUMA KARANTA: Ranar Nelson Mandela: Babban Jamiin MƊD ya yi ƙira da a ɗauƙi matakin magance talauci da rashin daidaito
Rahoton ya ƙara da cewa a shekarar da ta gabata mutum biliyan 1.1 cikin mutane biliyan 6.1 a fadin ƙasashe 110 na fuskantar matsanancin talauci.
Sannan ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 584 ‘yan kasa da shekaru 18 ne ke fama da matsanancin talauci, wanda ya kai kashi 27.9 na yara a duk duniya, idan aka kwatanta da kashi 13.5 na manya.
Har ila yau, ya nuna cewa kashi 83.2 cikin 100 na matalautan duniya suna zaune ne a yankin kudu da hamadar Saharar Afirka da kuma Kudancin Asiya. Sabina Alkire, daraktar hukumar OPHI, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa rikice-rikice na kawo cikas ga ƙoƙarin rage radadin talauci.
“A wani mataki, waɗannan binciken suna da kyau. Amma abin da ya ba mu mamaki shi ne yawan mutanen da ke fama da rayuwa mara kyau kuma a lokaci guda suna tsoron kare lafiyarsu – sun kai miliyan 455,” in ji ta.
Alkire ta ƙara da cewa, “Wannan yana nuni da wani babban ƙalubale da ke gaban ƙasashen duniya na ganin sun yi ƙoƙarin rage raɗaɗin talauci da kuma samar da zaman lafiya, ta yadda duk wata salama da za ta biyo baya ta ɗore.”
Indiya ita ce kasa mafi yawan mutane da suke cikin matsanancin talauci, lamarin da ya shafi mutum miliyan 234 daga cikin biliyan 1.4 na al’ummarta.
Sai kuma Pakistan da Habasha da Nijeriya da kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Rabin mutum biliyan 1.1 da suke cikin tsananin talauci a duniya suna kasashen nan biyar.