Mutum 3 da suka yi yunƙurin kashe ɗan sanda sun shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar, 31 ga watan Disamban 2022, ta kama wasu mutane uku da suka yi yunƙurin kashe wani ɗan sanda mai suna Sajan, Akinpelu Sunday, yayin da yake gudanar da aikinsa a Orile imo, da ke yankin karamar hukumar Obafemi Owode na jihar Ogun.

A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SO Abimbola Oyeyemi, waɗanda ake zargin; Olayiwola Basiru da Bamimore Isiaka da kuma Soliu, an kama su ne a lokacin da suka kai wa ɗan sanda hari tare da yunkurin kona motar ‘yan sandan don hana gudanar da bincike kan musabbabin haɗarin.

“Bayan rahoton wani hatsarin da ya afku a unguwar Orile imo, wani Sajan ɗan sandan da ke aiki da sashin kula da zirga-zirgar ababen hawa na ofishin ‘yan sandan da ke Owode Egba ya yi cikakken bayani don ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da ƙwato motocin da suka rutsa da su zuwa ofishin ‘yan sandan.

KU KUMA KARANTA:‘Yan sanda sun ƙwato naira miliyan 262 daga masu garkuwa da mutane cikin shekaru uku

“Amma da isa wurin, waɗanda ake zargin sun afkawa ɗan sandan da direban motar da guduma da sauran muggan makamai domin hana su ɗauki ɗaya daga cikin motocin da abin ya shafa zuwa ofishin domin ci gaba da bincike.

“Ɗan sandan da direban motar da ya ja motar sun yi nasarar tserewa daga wurin inda suka garzaya ofishinsu da raunuka daban-daban da mutanen suka yi masu” in ji Abimbola Oyeyemi.

Ya ce DPO ’yan sanda na sashen Owode Egba, CSP Olasunkanmi Popoola a ya jagoranci mutanensa zuwa inda lamarin ya abku, inda ya gana da waɗanda ake zargin da suka rigaya suka zuba man fetur suna yunƙurin ƙona motar da ke jan motar, bayan kwashe kuɗin da suka yi, wadanda yawansu ya kai N520,000 mallakin direban motar da aka kai domin janye motar.

“Uku daga cikin ɓarayin da ake zargin sun shiga hannu, yayin da wasu suka tsere, an kuma ƙwato man fetur daga hannunsu wanda suka yi yunƙurin ƙone motar da shi” in ji shi.

A halin da ake ciki kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Lanre Bankole ya bayar da umarnin cewa dole ne a nemo waɗanda suka tsere tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Ya kuma bayar da umarnin a miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *