Mutum 17 sun jikkata yayin da wasu ‘yan daba suka kai hari kan ɗan takarar sanatan APC a Kano

Aƙalla mutane 17 ne suka sami raunuka daban-daban a ranar asabar ɗin da ta gabata yayin da wasu ‘yan daba suka kai hari kan ayarin motocin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar kujerar sanatan kano ta tsakiya a jam’iyyar APC mai mulki, Abdussalam Abdulkarim a ƙauyen Gayawa da ke jihar Kano.

Wani ganau ya ce ɗan takarar mai suna AA Zaura da ƙyar ya tsallake rijiya da baya, saboda an lalata motocin yaƙin neman zaɓensa sama da 10.

Mai taimaka wa AA Zaura kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Mua’azzam, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da suke dawowa daga ziyarar jaje.

“Ƙididdigar da muka yi,akan ɓarnar da wannan mummunan aiki ya haddasa, ya zuwa yanzu mun gano ƙananan yara 17 da suka jikkata.

KU KUMA KARANTA:‘Yan daba sun kaima ‘yan majalisar Bauchi hari

“Waɗanda suka jikkata sosai,suna jinya a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, muna kuma da motoci 17 da suka lalace,” inji sh.

A halin da ake ciki, darakta janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen AA Zaura, Yahaya Adamu Garin Ali, a cikin ƙarar da ya shigar ranar 17 ga watan disamba ya buƙaci kwamishinan ‘yan sandan da ya yi cikakken bincike.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *