Mutum 129 sun mutu, sama da 120 suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa

0
110
Mutum 129 sun mutu, sama da 120 suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa

Mutum 129 sun mutu, sama da 120 suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa

Mummunan iftila’in ambaliyar ruwa a Nijar ya yi sanadin mutuwar mutane da dama yayin da wasu kuma suka jikkata tun da aka shiga lokacin daminar bana a ƙasar.

Hukumar shirye-shirye da gargadi da kuma takaita aukuwar bala’o’i tare da kare al’umma (DPA/GC) a Nijar, ta ce ya zuwa 12 ga watan Augusta, 2024 iftila’in ya yi sanadin mutuwar mutum 129, yayin da wasu mutum 126 kuma suka jikkata.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, al’ummomi 28,000 ne iftila’in ya shafa, yayin da gidaje 23,619 suka rushe sannan an yi asarar dabbobi 16,000, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Actuniger ta rawaito.

Yawan adadin da ɓarnar ta haifar ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da adadin da ministar ayyukan jinƙai da takaita aukuwar bala’o’i a Nijar, Madam Aissa Laouan Wandarama ta bayyana ya zuwa ranar 7 ga watan Agusta.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa a Jigawa tayi sanadiyar mutuwar mutane 16 tare lalata gidaje da dama

Rahoton bayanan da aka tattaro a lokacin ya yi nuni da cewa, mutum 94 ne suka mutu, daga ciki an rasa 44 daga kai-tsaye sakamakon ambaliyar ruwan, yayin da 50 kuma suka mutu a ruftawar gidaje.

Kazalika adadin mutanen da lamarin ya shafa a lokacin ya kai 137,156, inda gidaje 14,045 suka rushe sai kuma ɓukkoki 502 sun lalace.

An kuma yi asasar dabbobi 15,470, daga ciki akwai ƙananan dabbobin gida 13,981 da kuma manya 297.

Sannan ambaliyar ta shafe kadada 2,763 na gonakin noma a Nijar, inda aka yi asarar ton 17,495 na kayan amfanin gona tare da jikkata mutane 93.

Rahotannin baya-bayan nan dai sun nuna yadda iftila’in ya haifar da mummunar barna a kusan dukka faɗin yankunan Nijar, inda ta shafi ababen more rayuwa tare da katse hanyoyin tafiye-tafiye a ƙasar.

Ƙididdigar hasashen yanayi ta yi nuni da cewa akwai yiwuwar iftila’in ambaliyar ruwa a shekarar 2024 a yankunan Yammaci da tsakiyar Afirka ya zarce na shekarun baya.

Ta kuma ce hakan zai ta’azzara yanayin da al’ummomi ke ciki matuƙar ba a ɗauki matakan da suka kamata ba bisa ga tsarin kariya da muhimman matakan takaita tasirin sauyin yanayi da hukumomi suka bayar.

Leave a Reply