Mutum 11 a Uganda sun mutu bayan fashewar tankar mai
Aƙalla mutum 11 ne suka mutu a ranar talata bayan da wata motar ɗaukar man fetur ta fashe a kusa da hanya a Uganda, a cewar ‘yansanda.
Motar ta kife bayan wani hatsari, sannan daga bisani ta fashe a wani gari da ke kusa da Kampala, babban birnin ƙasar, kamar yadda kakakin ‘yansanda Patrick Onyango ya bayyana.
Wani bidiyo da wani mai kallo ya wallafa a intanet ya nuna yadda mutane ke ɗiban man daga cikin motar kafin ta yi bindiga.
Wannan mummunan yanayi kamanceceniya da wanda ya faru a Najeriya makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 140, ciki har da yara ƙanana.
Mutanen da ke hanzarin zuwa wurin don tattara man fetur daga motocin da suka sami hatsari na fatan siyar da shi, duk da gargaɗin da ake yi musu su nisanci irin wadannan wuraren.
KU KUMA KARANTA: Faɗuwar tankar mai a Jigawa, mutane 94 sun ƙone ƙurmus, 50 sun samu raunuka
An samu irin waɗannan al’amura da dama tsawon shekaru a yankin Gabashin Afirka.
Akalla mutum 62 ne suka mutu a Tanzania a shekarar 2019 yayin da suka yi ƙoƙarin zubar da mai daga wata motar da ta samu matsala.
A Kudancin Sudan, aƙalla mutum 183 ne suka mutu a shekarar 2015 lokacin da ɗaruruwan mutane suka taru a kusa da wata motar ɗaukar man fetur domin tattara man.









