Mutane sama da 48 suka mutu a mahaƙar zinare a Mali

0
20
Mutane sama da 48 suka mutu a mahaƙar zinare a Mali

Mutane sama da 48 suka mutu a mahaƙar zinare a Mali

Mali na ɗaya daga cikin ƙasashe da ke kan gaba wajen samar da zinare a nahiyar Afirka, kuma wuraren hakar ma’adinai a kai a kai ne ake samun mummunar zaftarewar kasa da kuma hadurra.

Hukumomin kasar sun yi ta fadi tashin hana yadda ake hako karafa masu daraja a kasar ba bisa ka’ida ba, wadda ke cikin kasashe mafi talauci a duniya.

Majiyar dan sandan yankin ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 48 biyo bayan zaftarewar kasa.

Wadanda abin ya shafa dai ‘yan mata ne, ciki har da wadda ke dauke da dan ta a baya.

Boubacar Keita, na kungiyar masu neman zinare ta Kenieba, shi ma ya kidaya akalla gawarwaki 48.

KU KUMA KARANTA:Kaiwa Ga Al’umman Da Suka Fi Buƙata A Najeriya: Tsarin bayar da agajinmu a 2025 – Mohammed Malick Fall

Shugaban wata kungiyar kare muhalli a yankin ya shaida wa kamfanin dillanci labaran Faransa cewa “Wurin ana gudanar da shi ba bisa ka’ida ba. Akwai matsala mai yawa a cikin cin gajiyar irin wannan rukunin wuri a yankin.” Ya kuma kara da cewa ana ci gaba da neman wadanda abin ya rutsa da su.

Hatsarin na ranar Asabar ya faru ne a wani wuri da ada kamfanin kasar Sin ke aiki da ya yi watsi da shi, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP.

A watan Janairu da ya gabata, wata zaftarewar kasa a wata mahakar zinare da ke kudancin kasar Mali ta kashe akalla mutum 10 tare da bacewar wasu da dama, wadanda yawancin su mata ne.

Sama da shekara guda da ta gabata, wani ramin karkashin kasa ya rufta a wani wurin hakar zinare a yankin da zaftarewar kasa ta faru a ranar Asabar, inda mutum sama da 70 suka mutu.

Leave a Reply