Mutane 4 sun mutu a Borno sakamakon kifewar wani kwale-kwale

0
77
Mutane 4 sun mutu a Borno sakamakon kifewar wani kwale-kwale

Mutane 4 sun mutu a Borno sakamakon kifewar wani kwale-kwale

An tabbar da rasuwar aƙalla mutane huɗu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar hukumar Dikwa da ke Jihar Borno.

Kakakin ’yan sanda a jihar, ASP Kenneth Daso, ya sanar a ranar Talata, cewa “hatsarin kwale-kwale ya afku a ranar 23 ga watan Satumba, 2024 a yankin Bakassi da ke tsakanin Mafa da Dikwa a kan hanyar Maiduguri, inda ya yi sanadin asarar rayukan mata huɗu.

“Waɗanda suka mutu, dukkansu ’yan unguwar Bulabulin, Dikwa, kuma an gano su, an kai su babban asibitin Dikwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

KU KUMA KARANTA: Mutane 35 sun ɓace a cikin ruwa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Zamfara

“Daga bisani an miƙa gawarwakin ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”

Kwamishinan ’yan sandan jihar, ML Yusufu, a yayin jajantawa, ya buƙaci mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, da su yi taka-tsan-tsan a wannan lokaci, tare da gaggauta kai rahoton duk wani lamari na gaggawa.

Leave a Reply