Muna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bindiga suka sace – Gwamnatin Kogi

0
70

‘Yan bindigar dai sun aukawa jami’ar kimiyya da fasaha ne dake garin Osara a ƙaramar hukumar Adabi a jihar Kogi inda bayan jikkata wasu ɗaliban, sannan suka yi garkuwa da wasu kimanin 57.

Malam Ɗan Asabe wani mazaunin jihar Kogi yace ‘yan bindigar sun haura cikin jami’ar ne ta baya suka dinga harbin kan mai uwa da wabi kamar yadda ya yiwa wakilin Muryar Amurka bayani ta wayar salula.

Tuni dai Gwamnatin jihar Kogin ta yi Allah wadai da wannan hari tare da nuna takaicinta akan lamarin.

Kwamishinan Labarai na jihar Kogin, Kensly Fanwo, yace, kawo yanzu ba su tantance adadin ɗaliban da ‘yan bindigar suka sace ba, amma sun haɗa hannu da jami’an tsaro domin ganin an kuɓuta da ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

KU KUMA KARANTA:’Yan bindiga sun sace ɗalibai a Jami’ar Jihar Kogi

Ya ƙara da cewa, a lokacin da gwamnatin jihar ta samu labarin ta yi ƙoƙarin jibga jami’an tsaro a wannan yanki domin samun nasarar kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

A wata sanarwa daga kakakin ‘yan sandan jihar Kogin, Wilyans Aya, ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin samun nasarar kuɓutar da ɗaliban.

Garkuwa da ɗaliban makaranta dai na ci gaba da ɗaukar hankali a Nijeriya, al’amarin da masana suka ce babbar barazana ce a ɓangaren Ilimi a ƙasar.

Leave a Reply