Muna ƙoƙarin ganin an rage kuɗin Hajjin 2025 – NAHCON

0
40
Muna ƙoƙarin ganin an rage kuɗin Hajjin 2025 – NAHCON
Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman.

Muna ƙoƙarin ganin an rage kuɗin Hajjin 2025 – NAHCON

Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce hukumar na aiki tuƙuru don ganin an rage kuɗin Hajjin 2025, wanda ake tunanin zai kai kusan Naira miliyan 10.

Duk da cewa ba a sanar da kuɗin a hukumance ba, hukumar ta tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta bai wa maniyyata tallafi ba a yayin aikin Hajjin 2025.

Rahotanni sun nuna cewa cire tallafin na iya sa kuɗin Hajji ya kai Naira miliyan 10 idan canjin Dalar Amurka ya tafi a kan Naira 1,650.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Shugaban NAHCON ya bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin ganin an rage kuɗin da za a biya domin aikin Hajjin 2025.

Ya ce, “Da farko, wannan ba shi ne burinmu ba, kuma ba shi ne abin da muke so ya faru ba.
“Babu wata sanarwa game da hakan. Abin da muke yi shi ne mu tabbatar cewa kuɗin bai kai haka ba, kuma muna sa ran da taimakon Allah hakan ba zai faru ba.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ƙaryata rahotanni kan ƙin fitar Alhazan Najeriya da dama daga Saudiyya

“Burina shi ne na tabbatar an samu ragi game da kuɗin idan aka kwatanta da wanda aka biya a bara, kuma a kan hakan muke aiki dare da rana.

“Muna da fata da kuma tabbacin cewa za mu samu nasara da taimakon Allah.”

Da aka tambaye shi game da dakatar da ayyukan da suka shafi Hajji daga Ƙungiyar Masu Kula da Aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHOUN), ya ce lokacin da lamarin ya faru ba ya hukumar.

Farfesa Saleh ya ce, “Duk da cewa ba na ofis a lokacin da aka sanar da dakatarwar, amma na gayyace su don tattaunawa kuma mun zauna muka yi magana har muka cimma matsaya.
“Mun fahimci buƙatunsu kuma za mu yi duk mai yiwuwa don ganin mun magance matsalar.

“Batun cewa ba za su halarci aikin Hajjin 2025 ba – ina ganin za a iya cewa an warware wannan matsalar. Mun yi taro da su, ni na jagoranci taron.

“Kuma sun ba mu shawarwari kan abin da suka ga ya kamata a yi domin warware matsalar, kuma za mu yi aiki a kai, in sha Allah.”

Leave a Reply