Connect with us

Kasashen Waje

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Published

on

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

Click to comment

Leave a Reply

Kasashen Waje

Shugaban Bangladash na riƙon ƙwarya ya yi ƙiran da a kai zuciya nesa

Published

on

Shugaban Bangladash na riƙon ƙwarya ya yi ƙiran da a kai zuciya nesa

Shugaban Bangladash na riƙon ƙwarya ya yi ƙiran da a kai zuciya nesa

Yunus mai shekaru 84, da ya taɓa lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi, da ke fuskantar babban ƙalubale na kawo ƙarshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen dimokuraɗiyya.

A jiya Asabar shugaban riƙon ƙwarya na Bangladesh Muhammad Yunus ya yi ƙira ga samun haɗin kan addinai bayan ganawa da mahaifiyar ɗalibar da ‘yansanda suka harbe har Lahira, lamarin da ya janyo zanga-zangar da ta kawo ƙarshen mulkin Sheikh Hasina na tsawon shekaru 15.

Yunus mai shekaru 84, da ya taba lashe lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi, da ke fuskantar babban kalubale na kawo karshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen demokradiyya.

Ya shaida wa manema labarai cewa “Hakinmu shi ne gina sabuwar Bangladesh,”

Hare-haren ramuwar gayya da aka kai kan mabiya addinin Hindu tsiraru a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin Hasina, ya haifar da fargaba a makwabciyar kasar Indiya da kuma fargaba a cikin gida.

A yayin wata ziyara da ya kai birnin Rangpur da ke arewacin kasar, Yunus ya yi kira da a kwantar da hankali, ta hanyar tunawa da karrama Abu Sayeed, dalibi na farko da aka kashe a rikicin na watan jiya.

KU KUMA KARANTA:Firaministar Bangladesh, Sheikh Hasina, ta sauƙa daga mulki

Ya kara da cewa “Abu Sayeed yanzu yana cikin kowane gida, yadda ya tsaya muma haka muke yi”. “Babu bambance-bambance a Bangladesh ta Abu Sayeed.”

A ranar 16 ga watan Yuli ne ‘yan sanda suka harbe Sayeed, mai shekaru 25, sa’adda ‘yan sanda suka fara kai farmaki kan masu zanga-zangar da dalibai suka jagoranta ta kin jinin gwamnatin Hasina.

Hasina, mai shekaru 76, ta fice daga kasar da jirgin sama mai saukar mai saukar ungulu zuwa makwabciyar kasar Indiya a ranar Litinin, yayin da masu zanga-zangar suka mamaye titunan Dhaka a wani gagarumin yunkurin kai karshen mulkinta.

Ana zargin gwamnatinta da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan gillar da aka yi wa dubban abokan hamayyarta na siyasa.

Continue Reading

Kasashen Waje

Ukraine ta kai ƙazamin hari kan yankunan iyaka na Rasha

Published

on

Ukraine ta kai ƙazamin hari kan yankunan iyaka na Rasha

Ukraine ta kai ƙazamin hari kan yankunan iyaka na Rasha

Dakarun Ukraine sun kai farmaƙi a yankunan kan iyakar da safiyar Talata, a wani hari da ya kasance mafi girma da samun nasara da Kyiv kai a cikin shekaru 2 da rabi na yaƙin.

Rasha ta fada jiya Asabar cewa ta kwashe dubban mutane daga yankin kan iyakarta, tare da ƙaddamar da farmakin yaƙi da ta’addanci, a daidai lokacin da take ƙoƙarin shawo kan wani babban kutse na Ukraine.

A lokaci daya kuma, Moscow ta yi gargadin cewa fadan da ake gwabzawa a yankin Kursk da ke yammacin kasar Rasha na yin barazana ga wata tashar makamashin nukiliya.

Dakarun Ukraine sun kai farmaki a yankunan kan iyakar da safiyar Talata, a wani hari da ya kasance mafi girma da samun nasara da Kyiv kai a cikin shekaru 2 da rabi na yakin.

Dakarun ta sun dada matsawa gaba da tazarar kilomita da dama, lamarin da ya tilastawa sojojin Rasha yin gaggawar waiwayar wurin ajiyar makamai da karin kayan aiki, ko da yake babu wani bangare da ya ba da cikakken bayani kan adadin sojojin da aka sanya.

KU KUMA KARANTA:Ƙasar Mali ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan ‘yan ta’adda

Jami’an yankin sun yi cikakken bayani kan yadda fararen hula da sika fice daga garuruwa da kauyukan da ke kusa da yankin da ake gwabzawa.

Sama da mutane 76,000 ne aka kwashe su na wucin gadi zuwa wasu wuraren tudun mun tsira,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na gwamnati TASS, ya ruwaito wani jami’in ma’aikatar kula da ayukan gaggawa na yankin yana fada a wani taron manema labarai a jiya Asabar.

An kai agajin gaggawa zuwa yankin kan iyaka, an kuma sanya karin jiragen kasa zuwa babban birnin kasar, Moscow, ga mutanen da suka arce wa yakin.

Amma da yammacin ranar Asabar ɗin, an yi ta harbe-harbe ta sama a Kyiv, babban birnin ƙasar Ukraine.

Continue Reading

Kasashen Waje

Mutane 9 ne suka mutu a rikicin ‘yan bindiga a Libya

Published

on

Mutane 9 ne suka mutu a rikicin ‘yan bindiga a Libya

Rikicin ya samo asali ne daga yunƙurin kashe Al-Baqra da aka yi a ranar Juma’a, wanda mayaƙansa suka ɗaura alhakinsa kan al-Shahida Sabriya, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka rawaito.

Jami’ai a kasar Libiya sun ce fadan da aka gwabza tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga masu dauke da manyan makamai a babban birnin kasar ya firgita mazauna yankin tare da kashe mutane kusan dozin daya, tashin hankali na baya bayan nan a wannan kasa ta arewacin Afirka da mafi yawanta babu doka da oda.

Jami’an sun kara da cewa, fadan da aka shafe sa’o’i ana gwabzawa, wanda ya hada da manyan makamai, ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Tajoura da ke gabashin birnin Tripoli ko Turabulus, tsakanin mayakan Rahba al-Duruae, karkashin jagorancin jagoran yaki Bashir Khalfallah, wanda aka fi sani da al-Baqrah, da kuma wata kungiyar ‘yan bindiga ta al-Shahida Sabriya.

Sashen Motocin Daukar Marasa Lafiya da Ayyukan Gaggawa na Ma’aikatar Lafiyar kasar ya ce akalla mutane 9 ne suka mutu, sannan wasu 16 suka jikkata a rikicin da aka kwashe sa’o’i ana yi.

Rikicin ya samo asali ne daga yunkurin kashe al-Baqra da aka yi a ranar Juma’a, wanda mayakansa suka daura alhakinssa kan al-Shahida Sabriya, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

Khaled al-Meshry, wanda shi ne sabon shugaban majalisar gudanarwar kasar da ke yammacin kasar, ya yi Allah wadai da yunkurin kisan gillar da aka yi, tare da yin kira da a gudanar da bincike domin hukunta wadanda suka aikata laifin.

KU KUMA KARANTA:Libya ta kora ‘yan Najeriya da Mali 463 Zuwa Nijar

Bangarorin biyu da ke gaba da juna suna kawance da gwamnati Firai minista Abdul Hamid Dbeibah.

Sai dai kakinta bai amsa bukatar yin magana kan lamarin ba.

Tashin hankalin dai ya nuna raunin kasar Libiya bayan boren da aka yi a shekarar 2011, da ya rikide ya koma yakin basasa, wanda ya kifar da gwamnatin Moammar Gadhafi da ya dade yana mulki kama karya.

Yayin da ake cikin rikicin, mayaƙan sun samu ƙaruwar dukiya da iko, musamman a Tripoli da yammacin ƙasar.

Continue Reading

You May Like