Mun yi ta jiran motar bas na tsawon sa’o’i bakwai – Ɗaliban Najeriya da ke Sudan

“Har yanzu muna ci gaba da fata,” in ji wata ɗaliba ‘yar Najeriya mai shekaru 22 a Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan, wanda ke jiran wata motar bas tun karfe 6:00 na safe domin ta samu ta tsere daga birnin.

Zafin rana a can na iya kai wa maki 43 na ma’aunin celcius, inda kuma ake fuskantar wahala wajen samun ruwan sha.

Sai dai, duk da haka ta ce ‘yan Najeriya da dama na jira a waje cikin zafin rana don tabbatar da cewa ba su rasa damar komawa gida ba.

A ranar Talata ne shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen ketare ta shaida wa wani shirin BBC cewa za a fara kwashe ‘yan ƙasar daga yau Talata.

KU KUMA KARANTA: Ɓangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun amince da tsagaita buɗe wuta

Da aka tambayi hukumar ta NDC kan dalilin da ya sa hukumomin Najeriya suka ɗauki tsawon lokaci wajen bayyana shirin kwashe mutanen, ta ce sai da suka samu izini daga ɓangarorin biyu na soja domin samun hanyar wucewa lafiya.


Comments

2 responses to “Mun yi ta jiran motar bas na tsawon sa’o’i bakwai – Ɗaliban Najeriya da ke Sudan”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Mun yi ta jiran motar bas na tsawon sa’o’i bakwai – Ɗaliban Najeriya da ke Sudan […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Mun yi ta jiran motar bas na tsawon sa’o’i bakwai – Ɗaliban Najeriya da ke Sudan […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *