Mun kama mutane 2,425 a Kano da zargin aikata laifuka a shekarar 2024 – ‘Yansanda

0
38
Mun kama mutane 2,425 a Kano da zargin aikata laifuka a shekarar 2024 - 'Yansanda

Mun kama mutane 2,425 a Kano da zargin aikata laifuka a shekarar 2024 – ‘Yansanda

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta samu nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka 2,425 tare da kwato muggan makamai, ƙwayoyi da kuma kayan sata daga ranar 1 ga watan janairu zuwa Disamban 2024.

kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yin ƙarin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a shekarar da mukai bankwana da ita.

CP Dogo, ya ce a farkon shekarar 2024, an yi fama da yunƙurin ‘yan bindiga masu shigowa jahar wanda suke da ƙananan hukumomi 17 akan iyakokin jahohin, Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi.

Haka zalika akwai kuma barazanar faɗan daba da kuma masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙananan hukumomin 8 na ƙwaryar birnin Kano.

Sai ƙananan hukumomi 19 waɗanda basa cikin birni ko kan iyaka , da aka samu yawan sace-sace da faɗa tsakanin makiyaya da manoma.

Kwamishinan ‘yansandan ya ƙara da cewa, kamar yadda babban sufeton yan sandan Nigeria, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ba da umarni tare da sanya su a kan hanya don ganin an faɗaɗa bada tsaro, a ƙasarnan gaba daya waɗanda suma a jahar kano ba a barsu a baya ba, inda suka kalli matsalar jahar, har suka ɗauki matakan magance matsalar musamman wajen kara inganta aikin tsaro da al’umma da bibiya a duk lokacin da suka samu bayanan sirri na yunƙurin shigowar ‘yan ta’adda suna kai ɗaukin gaggawa tare da sauran gamayyar hukumomin tsaro.

KU KUMA KARANTA: An kama masu laifi 30,000 a 2024 – ;Yansanda

Ya ce an kuma sake ƙarfafa tattara bayanan sirri da ƙara faɗaɗa sintiri a lungu da saƙo, don tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’ummar jahar.

Cikin nasarorin da rundunar ta samu sun hada da cafke ‘yan fashi da makami 189, masu garkuwa da mutane 34, barayin shanu 10, masu safarar bindigu 2, barayin motoci 22, dilolin kwaya 58, masu fasa kaurin mutane 18, ɓarayin adaidaita sahu 46 da kuma ɓarayin babura 28.

Sannan an cafke masu buga takardun bogi 4, yan damfara 27 da kuma ‘yan daba 1,987.

CP Salman ya ce sun tseratar da mutane 40 da aka yi safararsu da kuma kubutar da mutane 18 waɗanda aka yi garkuwa da su , sai mutane 2 da aka sace.

Haka zalika rundunar ta kwato bindiga ƙirar AK-47 guda 7, Beretta Pistol 1, Pump Action 4, Bindigar harbin tsintsaye 7, ƙirar gida 4 da kuma bindigar wasan yara 4.

Sannan an ƙwato harsasai 1,213, Adduna 57, Wukake 198, motoci 12, babura 44, adaidaita sahu 15, kuɗin jabu naira biliyan 129 da miliyan 542 da dubu 823 na kuɗaɗen ƙetare da kuma na Nigeria.

An ƙwato shanun sata 308, ATM Card 65, wayoyin sata 415, zoben azurfa 67, baturan sola 34 da kuma allurar 105.

A ƙarshe rundunar ta godewa gwamnatin jahar Kano, sauran hukumomin tsaro, ƙungiyoyin al’umma, ‘yansandan kwansitabulari, yan bijilanti , PCRC da kuma kafafen yaɗa labarai da wakilansu bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a musamman akan abunda ya shafi tsaro.

Leave a Reply