Mun kama mahaifin da ya zana wa ɗansa jarrabawa — JAMB

0
118

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Neman Samun Gurbin Karatu a Makarantun Gaba da Sakandare ta JAMB, Farfesa Ishaƙ Oluyede ya koka kan yadda wasu iyaye ke zana wa ‘ya’yansu jarabawar.

Shugaban na JAMB ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kaɗan bayan ya duba wata cibiyar zana jarrabawar da ke Kaduna a ranar Laraba.

Farfesa Oloyede ya ce kwanan nan an kama wani mahaifi da ya zana wa ɗansa jarabawar.

Oloyede ya ce, hakan ya zama babban ƙalubale ga hukumar, yana mai cewa masu yin zamba su sani hakan ba riba ce.

Ya kuma bayyana cewa, fasahar jarabawar na taimaka wa hukumar wajen duba irin waɗannan mutane tare da kama su.

“A duk faɗin ƙasar nan, galibin matsalar da muke fuskanta ita ce yin sojan gona.

“Muna da shari’ar uban da ya yi wa ɗansa sojan gona ya zana masa jarrabawa.

“Shin babu mamaki a wannan lamari, shin ba ka lalata makomar ɗanka ba kuwa?

“Tabbas, biyu daga cikinsu suna tsare. Ba zan iya fahimtar abin da uban zai gaya wa ɗansa ba lokacin da suke kulle a cikin sel ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya biya wa ɗalibai 6,500 kuɗin JAMB ‘yan asalin jihar Kano

“Wannan lamari ba shakka bai faru a Kaduna ba kaɗai, amma ba na son bayyana jihar.

“Don haka, galibin shari’o’in sojan gona ne, amma muna ci gaba da sauke nauyin da rataya a wuyanmu a kan lamarin.

“Kuma su ma waɗanda muka bari na bincike, za su ga abin da zai biyo baya bayan jarrabawar,” inji shi.

Shugaban ya ƙara da cewa, akwai wasu mutane da ke da lamba ta shaidar ɗan ƙasa NIN guda biyu da suka saɓa manufar tantance su.

Ya ce, hukumar za ta kai ƙarar Hukumar Kula da Shaidar Zama Ɗan Kasa (NIMC).

Leave a Reply