Mun gano yadda ake amfani da sunan mu a nemi kwangilar kama masauƙai da abinci a Saudia — NAHCON

0
33
Mun gano yadda ake amfani da sunan mu a nemi kwangilar kama masauƙai da abinci a Saudia — NAHCON

Mun gano yadda ake amfani da sunan mu a nemi kwangilar kama masauƙai da abinci a Saudia — NAHCON

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta ce ta gano yadda wasu ɓatagari ke amfani da sunan ta wajen nemo kwangilar kama masauƙai da ciyar da alhazai a Saudi Arebiya.

Hukumar ta ƙara da cewa waɗannan ɓatagari har ta’addar ta su ta kai su ƙulla yarjejeniya da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudi Arebiya da sunan NAHCON.

Wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Talata ta ce Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman bai sahalewa wasu kowani ko kamfanoni su ƙulla yarjejeniya da ƙasar Saudiyya don aikin Hajjin 2025 ba.

KU KUMA KARANTA:Muna ƙoƙarin ganin an rage kuɗin Hajjin 2025 – NAHCON

A cewar sanarwar,, NAHCON na kulla yarjejeniyar ta da gwamnatin Saudiyya ne ta hanyoyin da su ka dace kuma wanda kasar ta saka da su.

“Duk wata yarjejeniya da aka shigar, ba tare da sa hannu da sahalewar shugaban NAHCON ba da kuma shigar ma’aikatan NAHCON kai tsaye cikin harkar to ba sahihiya ba ce,” in ji Usara

Sanarwar ta ce duk mai wani neman sani ko tambayoyi kan aiyukan NAHCON ka iya zuwa kai tsaye domin ƙarin bayani.

Leave a Reply