Mun Gamsu Da Ayyukan Da El-Rufa’i Ya Shimfida A Kaduna- Inji Aminu Rahama

0
365

Daga; Rabo Haladu, Kaduna.

DAN majalisar dokokin Jihar Kaduna Mai wakiltar mazabar Karamar hukumar MaKarfi a zauren majalisar Jihar, Aminu Ahmad Rahama, ya bayyana gamsuwarsa dangane da irin ayyukan da gwamnan Jihar Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i ya shimfida a Jihar a cikin shekaru shida da ya yi a kan kujerar gwamna Jihar.

Aminu Ahmad Rahama, ya ce al’ummar Jihar Kaduna suna alfahari da ayyukan ci gaba da gwamnatin APC a Jihar ta kawo wanda al’umma ba za su manta da gudunmuwar da Gwamna El-rufa’i ya kawo a Jihar baki daya ba.

Dan majalisar ya bayyana haka ne a jawabinsa yayin da kungiyar ‘yan jarida na Arewa suka karramashi da lambar yabo bisa gudunmuwar da ya kawo a mazabarsa na tallafawa al’umma.

Aminu Rahama, ya kara da cewa, duk kudurorin da gwamna yake aikowa majalisa; kudurorine na bunkasa ci gaban Jihar ne wanda hakan ya sanya ba a samun baraka tsakanin bangaren zartaswa dana majalisar Jihar. A cewarsa, sun gamsu da ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar take shimfidawa a ciki da wajen Jihar baki daya.

A cewar dan majalisar, Gwamna Nasir El-Rufai ya gina kuma yana ci gaba da gina ababen more rayuwa a Jihar Kaduna yana mai cewa ya kafa ma’auni masu girma wanda dole ne a tabbatar da cewa an kiyaye tare da kiyaye abubuwan more rayuwa da ya gina.

Ya ce “ya zama wajibi su bawa jagoransu kwarin gwiwa da ya ci gaba a yunkurin ganin Jihar Kaduna ta zama abin koyi na ci gaba a fadin kasar baki daya.”

Dan majalisar ya bukaci daukacin al’ummar Jihar dasu taimakawa kokarin Gwamnatin Jihar na samar da zaman lafiya a fadin Jihar wanda sai da zaman lafiya ci gaba zai kara samuwa.

A kan hakan, yace matsayinsu na wakilan al’ummar Jihar kuma masu tsara dokoki, za su yi iya bakin kokarinsu wajen samar da dokokin da zasu kawo ci gaba a Jihar, hasalima, zasu ci gaba da zama wakilai na gari a zauren majalisar Jihar.

Daga karshe, ya yaba da kokarin kafafen yada labarai wajen bayyanawa al’umma halin da kasa take ciki inda ya bukace dasu kaucewa yada labaran da zasu kawo rashin zaman lafiya a kasa baki daya.

Leave a Reply