Mummunar gobara ta jikkata mutane fiye da 80 a birnin Conakry

Aƙalla mutane 8 suka mutu, yayin da wasu 84 kuma suka jikkata sakamakon fashewar wani abu a wata tashar mai da ke Conakry babban birnin ƙasar Guinea a safiyar ranar Litinin ɗin nan.

Jami’in ɗan sandan da ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce adadin da suka bayar na mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin fashewar na wucin gadi ne, la’akari da cewar akwai yiwuwar ya ƙaru.

Bayanai sun ce gilasan tagogin gine-gine da dama da ke kusa da ma’adanar man sun fashe, yayin da ɗaruruwan mutane suka tsere, sakamakon fashewar da aka samu a tashar man fetur ɗin wadda ita ce irinta guda ɗaya tilo a Guinea, da ke gundumar Kaloum a tsakiyar Conakry babban birnin ƙasar.

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce ana iya hangen mummunar gobarar da tashi daga nisan kilomita akalla guda, yayin da jami’an kwana-kwana suka garzaya zuwa wurin, inda tuni wasu manyan motocin dako na tanka suka fice daga ma’ajiyar ta man fetur, tare da rakiyar sojoji da ‘yan sanda.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *