Mummunar gobara a Kano, ta ƙone shaguna 6 ƙurmus a kasuwar Kurmi

0
247
Mummunar gobara a Kano, ta ƙone shaguna 6 ƙurmus a kasuwar Kurmi

Mummunar gobara a Kano, ta ƙone shaguna 6 ƙurmus a kasuwar Kurmi

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewar wasu shaguna 6 sun kone kurmus, yayin da wasu biyar kuma suka lalace a sanadiyar wata gobara da ta afku a kasuwar kurmi ‘yan jagwal.

Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar ACFO Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar yau juma’a.

Ya ce hukumar a yau Juma’a 18 ga Afrilu 2025 da misalin karfe 01:35 ta samu kiran gaggawa daga baturen ‘yan sanda mai kula da Jakara, inda ya sanar cewar gobara ta tashi a kasuwar Kurmi, Jakara ‘yan Jagwal.”

Ya kara da cewar Jami’an hukumar sun kai daukin gaggawa kasuwar domin magance yaduwar zuwa wasu sassan kauswar da isar su sun gano cewa, wasu shagunan kasuwar shida, sun riga sun kone kurmus, yayin da wasu biyar kuma ke ci da wuta a dai-dai lokacin da suka isa.

KU KUMA KARANTA:Mummunar gobara a Kano ta jikkata yaro, ta janyo asarar dukiya mai yawa

“Cikin ikon Allah da isar mutanen mu kasuwar suka sami nasarar kashe gobarar ba tare da bata wani lokaci ba. Wanda hakan ya sa muka kare asarar dukiya mai yawa.” ACFO Saminu ya fada.

Haka kuma a cewarsa hukumar, ko a ranar talatar makon da ya gabata an sami gobara a kasuwar don haka za,a yi bincike a kan musabbabin afkuwar gobarar ”

Ya kara da cewar babu rauni ko kuma rasa rai a sakamakon gobarar.

Leave a Reply