Mulkin soja ya fi mana alheri a kan Dimokuraɗiyya – ‘Yan Nijar Mazauna Najeriya
A taro na musamman a ofishin jakadancin Nijar a Abuja don zaben sabbin shugabannin kungiyar ‘yan Nijar a Najeriya, jagororin kungiyar sun ce ‘yan siyasa ba su tabuka abun kirki ba don haka gara soja su daidaita kasar kafin dawo da mulkin hannun farar hula.
Du da haka ‘yan kungiyar karkashin jagorancin sabon shugaba Muhammad Tasi’u Kalgo sun ce su na zama lafiya a Najeriya ba tare da samun wata tsangwama ba duk da ficewar kasar su daga ECOWAS.
Shugaban kwamitin zaben kungiyar wanda har ila yau shi ne tsohon shugaban kungiyar Abubakar Khalidou ya ce gaaskiyar magana jagorancin shugaban soja na Nijar Janar Abdulrahman Tchiani na haifar da sabon ‘yancin kasar daga mamayar mulkin mallaka “mu so mu ka yi sojoji su yi shekaru 35 din da ‘yan siyasa su ka yi mu aza su a sikeli sau mu auna mu gani na way a fi kyau, amma yanzu mu dai ba ma goyon bayan siyasa”
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Nijar ta bawa baƙi takardun izinin zama
Sabon shugaban kungiyar Muhammad Tasi’u Kalgo ya ce su na daukar kan su tamkar ‘yan Najeriya kuma ba sa ma ganin sauyin madafun iko daga farar hula zuwa soja ya taba dangantakar Najeriya da Nijar “Nijar fa da Najeriya abu daya ne, kuma akwai yarjeniyoyi tun kafin kafa ECOWAS, dukkan mu’amala ta shige da fice da kasuwanci na cikin wannan yarjejeniya”
Da alamu ‘yan Nijar har ma da ‘yan siyasar su da ke da shugabanni a Najeriya ba sa sha’awar baiyana ra’ayi don yanda lamura su ka yi zafi a diflomasiyya amma duk da haka ‘yar kungiyar Zainab Muhammad Dezol ta ce ba amfanin caccakar juna don wataran za a yi zabe ko a ce dimokradiyya za ta dawo “gwamnati za ta zo gwamnati za ta tafi. Za a yi zabe za a zabo wasu sababbi daban. Za mu taru mu yi zaben gwamnatin da mu ke so, wani lokacin ta zo da wani abu da ba haka mu ka yi tunani ba amma mu (FAMI) ne”
Nijar da Najeriya duk ba bakin mulkin soja ba ne, amma a yayin da Najeriya ke nasarar shekara 26 da mulkin soja ba katsewa, Nijar, Mali da Burkina Faso sun koma mulkin soja da ba takamemmen lokacin dawowar farar hula don sojojin sun ma kafa kungiyar AES don tsarawa kan su muradun su da kaucewa katsalandan din ECOWAS.