No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta tabbatar da Muhammad Sani Abacha a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Alƙalin kotun mai shari’a A.M Liman a wani hukunci da ya yanke a yammacin ranar Alhamis ya soke zaɓen fidda gwanin da ya gabatar da Sadik Amunu Wali a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP tare da umartar INEC da ta cire sunansa, a maida na Muhammad Sani Abacha.

Kotun ta amince da dukkan ƙorafi na wanda ya shigar da ƙara a cikin takardar. Wanda ya shigar da ƙarar, Muhammed Sani Abacha yayin da INEC ke kare ɗayan wanda aka shigar ƙara, Sadik Aminu Wali na biyu, PDP na uku sai Wada Sagagi na huɗu.

Da yake tsokaci kan hukuncin, ɗaya daga cikin Lauyan mai ƙara, Barista Sai’du Tudunwada ya bayyana hakan a matsayin ingantaccen hukunci da nasara ga dimokuraɗiyya.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...