Morocco ta kafa tarihin zama ƙasar Larabawa da Afirka ta farko da ta tsallake zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya

Morocco ta doke Portugal a ranar Asabar, inda ta zama kasa ta farko ta Larabawa da Afirka da ta taɓa tsallakewa zuwa zagaye na hudu a gasar kwallon kafa ta duniya.

Tawagar kwallon kafar Morocco ta kafa tarihi a Qatar a ranar Asabar da ta gabata, inda ta lallasa Portugal sannan ta tsallake zuwa matakin wasan kusa da na karshe, na gasar cin kofin duniya, inda ta zama kasa ta farko ta Larabawa da Afirka da ta taɓa yin hakan a tarihin gasar.

An yi zaton Portugal za ta doke Morocco a wasan daf da na kusa da na karshe na FIFA a matsayi da ci 9 da 22, amma ‘yan wasan Morocco da aka fi sani da “Atlas Lions” sun samu nasara mai cike da tarihi da ci 1-0. Youssef En-Nesyri ne ya ci kwallon.

Ɗan wasan Morocco, Sofiane Boufal lokacin da ya ke murnar samun nasara tare da mahaifiyarsa

Fitaccen ɗan wasan Portugal Cristiano Ronaldo bai buga wasan farko ba, amma ya kasa kai wa tawagar kasarsa nasara a karo na biyu.

KU KUMA KARANTA:Yadda Croatia ta doke Brazil da bugun fanariti, ta kai wasan kusa da na ƙarshe

Ana kyautata zaton wannan shine gasar cin kofin duniya na ƙarshe da Ronaldo zai taka leda.
Ɗan wasan mai shekaru 37 na iya ƙulla yarjejeniya da kulob din Al-Nassr na Saudiyya nan ba da jimawa ba, wanda aka ce an yi masa tayin sama da dala miliyan 200.


Comments

One response to “Morocco ta kafa tarihin zama ƙasar Larabawa da Afirka ta farko da ta tsallake zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Morocco ta kafa tarihin zama ƙasar Larabawa da Afirka ta farko da ta tsallake zuwa wasan kusa da na… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *