Manyan hafsoshin tsaron Turkiyya da na ƙasar Djibouti ta gabashin Afirka sun sa hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi da ƙa’idoji a birnin Ankara, waɗanda suka haɗa da yarjejeniyar hadin gwiwa ta horar da sojoji, da yarjejeniyar hadin gwiwar hada-hadar kuɗi ta soji, da kuma yarjejeniyar aiwatar da tallafin kuɗi.
Ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa, a hukumance Minista Yasar Guler ya yi maraba da Ministan Tsaron Djibouti Hassan Omar Mohamed a ranar Litinin, wanda ya isa birnin Ankara a matsayin baƙo, tare da bikin soji. Bayan kammala bikin, ministocin biyu sun ci gaba da taron ƙasashen biyu.
Ma’aikatar ta ce a ƙarƙashin jagorancin hafsoshin tsaron biyu an gudanar da wani taro na matakin tawaga.
KU KUMA KARANTA: Turkiyya na fatan bunƙasa kasuwanci da Saudiyya zuwa dala biliyan 30
Ma’aikatar ta ce, a taron wanda ya samu halartar kwamandan rundunar sojin ƙasa ta Turkiyya Janar Selcuk Bayraktaroglu, hafsoshin tsaron sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi uku.
Ƙasar Djibouti mai yawan al’umma ƙasa da miliyan guda, tana wuni muhimmin yanki a Gaɓar Tekun Aden a matsayin hanyar wucewa ta Bahar Maliya.