Mbappe ba zai yi atisaye da PSG ba

1
258

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kylian Mbappe ba zai yi atisaye da tawagar ‘yan wasan Paris St-Germain ba a lokacin da suka ƙara shiri a ranar Litinin don fara gasar Ligue 1.

Mbappe dai ya kasance cikin takun-saƙa da kwantiragi da PSG a lokacin da yake son komawa Real Madrid.

Ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a raga a kulob ɗin ya ƙi amincewa ya tsawaita kwantiraginsa na shekara guda da zai ƙare a bazara mai zuwa.

Don haka PSG na son siyar da ɗan wasan gaban Faransa a yanzu domin su samu kuɗi a kansa a maimakon barinsa ya tafi a kyauta.

Sakamakon haka an cire Mbappe cikin tawagar PSG da ta yi balaguron tunkarar kakar wasa ta bana a nahiyar Asiya.

1 COMMENT

Leave a Reply