An bayyana ɗan takarar jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Mohammed Bello Shehu a matsayin wanda ya lashe zaɓen majalisar wakilai ta tarayya ta Fagge a jihar Kano.
Mallam Shehu ya doke ɗan majalisar wakilai mai ci, Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC, inda ya kawo ƙarshen mulkinsa na shekaru 12 a majalisar jihar Kano.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa MB Shehu ne ke kan gaba da ƙuri’u sama da 18,000 a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu kafin INEC ta ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba sakamakon soke wasu rumfunan zaɓe saboda tashin hankali.
KU KUMA KARANTA: Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, ya lashe kujerarsa
Da yake bayyana sakamakon sake zaɓen a ranar Asabar, jami’in zaɓen, Ibrahim Suraj, ya ce MB Shehu ya samu ƙuri’u 19, 024, sai ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Shuaibu Abubakar, wanda ya samu ƙuri’u 12,789 na jimillar ƙuri’u da aka kaɗa.
Suraj ya kuma bayyana cewa Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC ya zo na uku da ƙuri’u 8,669. “Wannan Barista M.B. Shehu na jam’iyyar NNPP, bayan ya cika sharuɗɗan doka kuma ya samu mafi yawan ƙuri’u an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen,” in ji jami’in zaɓen.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a ƙarashen zaɓen na yau, jam’iyyar NNPP ce ta jagoranci zaɓen da ƙuri’u 609, yayin da APC ta zo ta biyu da ƙuri’u 268, sai LP da ƙuri’u 60.
Sai dai a lokacin da aka taƙaita sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata, jam’iyyar NNPP ta zo ta ɗaya, sai LP, sannan APC.