Mayaƙan Al-Shabaab sun kashe wasu ƙauyawa biyar a yankin gaɓar tekun Kenya

1
307

‘Yan Kenya biyar ne aka kashe tare da ƙona gidaje bayan da mayaƙan al-Shabaab suka kai hari a wasu ƙauyuka biyu na lardin Lamu da ke gaɓar ruwan Kenya a yammacin ranar Asabar, kamar yadda ‘yan sanda da shaidu suka tabbatar a ranar Lahadi.

‘Yan sanda da shaidu sun ce maharan sun kai farmaki ƙauyukan ne da misalin ƙarfe 7:30 na dare a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ya jawo waɗanda abin ya shafa daga gidajensu, tare da ɗaure hannayensu da ƙafafu da igiya a bayansu kafin a kashe su.

A cewar rahoton ‘yan sanda waɗanda harin da aka kai daren Asabar a ƙauyukan Salama da Juhudi ya rutsa da su maza ne ciki har da ɗalibi ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun tarwatsa mayaƙan babban ɗan bindiga Boderi, shi kuma yasha da ƙyar

Shaidu sun ce ɗalibin ya dawo gida ne domin hutun rabin wa’adi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wasu mutane sama da 30 sanye da kayan sojoji ɗauke da bindigu, adduna, da kuma wuƙaƙe, sun kai hari da sanyin safiyar yau.

Daga nan sai suka umarci waɗanda suke wurin da su kwanta, ka da su ɗaga sauti yayin da suka kai mata ɗakuna daban-daban sannan daga baya aka sako su.

Maharan sun kashe mutanen biyar tare da sace wasu kayan abinci, kaji, da awaki kafin su ƙona wani shago.

“Maharani sun ɓace zuwa dajin,” in ji ‘yan sandan.

Kwamishinan Lamu, Louis Rono, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wurin da lamarin ya faru, amma ba a kama su ba.

Gundumar Lamu dai ta kasance cikin hasashe tsawon wasu shekaru saboda ƙaruwar munanan hare-haren da mayaƙan al-Shabaab ke kaiwa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbim jami’an tsaro da fararen hula.

1 COMMENT

Leave a Reply